‘Yan bindiga sun yi awon-gaba da wani alƙalin babban kotun Kebbi

Spread the love

Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR Birnin Kebbi

Mahukuntan babban kotun Jihar Kebbi sun tashi tsaye tare da haɗin gwiwan hukumomin tsaro domin ceto wani alƙalin kotun, Justice Faruq Hassan Bunza, wanda ‘yan bindiga suka wuce da shi daga gidansa dake Bunza da tsakar daren Asabar.

Rahotanni na nuna cewar Justice Faruq Bunza yayi tafiya zuwa maƙwabciyar Jihar Sokoto, a sa’ilin da ya dawo gida da sha-biyun dare, ya tarar da ‘yan bindiga na jiransa a ƙofar gidansa, a inda suka dinga aman-wuta da bindigogi ta sama, domin razana jama’a, daga nan kuma, suka wuce da alƙalin na babban kotu.

Tuni dai hukumomin babban kotun bisa jagorancin shugaban alƙalai na Jihar Kebbi, Justice Umar Abubakar, sun gana da hukumomin tsaron da suka wajaba, domin sha-ta dabarun ceto Justice Faruq Bunza, a dawo dashi cikin iyalinsa da ƙoshin lafiya.

By ukarofi

Leave a Reply