Gwamnatin Katsina ta jaddada ƙudirinta na cigaba da gyara makarantun da suka lalace

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnatin Katsina ta damu da labarin da wasu al’ummomi suka ɗora a soshiyal midiya kan lalacewar wata makaranta,hakan ya sanya gwamnati ta jaddada ƙudirin ta na gyara makarantu a faɗin jihar.

Kwanan nan gwamnatin jihar ta kammala gina makarantun sakandare guda 30 da wasu alƙawarin bada kwangilar wasu guda 49 a faɗin jihar.

Wata sanarwa ɗauke da sanya hannun kwamishinan Ilimi,Hon Yusuf Suleiman Jibiya, ya yaba wa alummomi da ke fitowa suna miƙa irin wannan buƙata tasu.

Kwamishinan ya tabbatar wa alummar cewa dama gwamnatin jihar ta sanya wannan makaranta cikin makarantun da gwamnati za ta bada kulawar gaggawa.

Hon Suleiman ya bayyana cewa rashin tsaro ya sanya aikin gyaran makarantun ya tsaya, a cewarsa, sai da gwamnati ta tabbatar da kare rayuka da dukiyar al’umma kafin ta fara shirye shirye na gyara makarantu.

“Yanzu zaman lafiya ya fara samuwa a yankunan,mutane sun fara komawa gidajen su,kasuwanni suna buɗewa haka ma makarantu da suka daɗe suna rufe an fara buɗewa wanda yasa gwamnati ta fara duba yiwuwar cigaba da ayyukan raya ƙasa,”inji Suleiman Jibiya.

Kwamishinan ya bayyana cewa gyaran makarantun sun haɗa da gyara azuzzuwa,canza rufin kwano,samar da kayan karatu da sauran su.

Ya ce jaddada ƙudirin gwamnatin Dikko Raɗɗa na bai wa harkar Ilimi fifiko ta hanyar inganta rayuwar malamai makaranta,samar da kayan karatu da ɗaukar matakin da ya dace na bunƙasa Ilimi a faɗin jihar.

Suleiman Jibiya ya yi kira ga alumma, hukumar makaranta da kwamintin kula da makarantu da su kare, tare da tsare gine ginen makarantu da kaddarorin gwamnati a yankunan su.

By ukarofi

Leave a Reply