Mu yi ƙorafi, kuma mu yi haƙuri

Daga RAHAMA ABDULMAJID

A gaskiya ana jin jiki daga sama har ƙasa, tashin dala, tashin abin masarufi, ƙarancin kuɗi, ƙaruwar talauci da yunwa. Ga kuma matsalolin tsaro, dole ‘yan ƙasa mu yi fushi, mu kuma harzuƙa, Yunwa da rashin tsaro abin tayar da hankula ne, babu mai ganin laifin wanda hankalinsa ya tashi saboda hakan. Don haka, wallahi ba ma ganin baikenku, hasali ma har yau ban taɓa shiga wani ɗakin taro a fadar shugaban ƙasa ba na ji ana zargin talaka don ya yi fushi ba. Sai dai ga shawarwari:

Ku yi ƙorafi:

Ƙorafi wani lokaci tamkar shawara ne ga mahukunta, tare da bayyana yanayin da mutum ya samu kansa, kuma yana rage raɗaɗi. Mu ma mun yi a baya don haka dole a mana, yana matuƙar taimakonmu fiye da cutar da mu.

Ku yi haƙuri:

Sai dai yaya za a yi? Dole mu ba ku haƙuri, ku yi haƙuri, mu yi haquri. Wallahi wallahi ana aiki babu dare babu rana, da a ce ba a aikin wallahi da ba za mu zauna a wurin ba ma. Don ko da ba ku yarda mun damu da ku ba, ku yarda da cewa mun san za mu gamu da Allah kuma muna tsoron hakan. Yanayin da Nijeriya ta samu kanta sakamakon sakacin da aka yi a baya dole sai an sha raɗaɗi a yayin ɗaukar wasu matakai da sauye-sauyen da za su iya kai ta ga farfaɗowa. Kuma a iya sanina da su shugaban ƙasa da mataimakinsa ke kwana su tashi

Ku yi watsi da jita-jita:

Ku bibiyi kafofin labarai na gaske maimakon na masu sharhi. Babu wani shiri na sauya birnin tarayya da ke gudana a yanzu a iya sanin mu, lalacewar mu ba ta kai ta a haɗa baki da mu a cutar da jama’a ba. Bari na muku wani fashin baƙi, Legas din kanta ba ta buqatar zama birnin tarayya a yanzu tunda ta gano irin ci gaban da za ta iya samu zai iya ɗorewa ne idan ba ta matsayin tarayyar ƙasa wanda kan mai da wuri na kowa da kowa. Jahar Legas na gasar zama babban birnin kasuwancin Africa ne ba na tarayyar Nijeriya ba, wannan ne tunanin ‘ya’yanta. Su kuwa ma’aikatun da aka mayar can ku bibiyi dalilai da tarihin yin hakan Ko ku bibiyi shafinmu na @Sabuwar Nigeria don samun labarin hakan.

Kyakkyawan fata:

Ƙwarai ana jin jiki amma mu yi hakuri za a farfazo, muna muku albishir da ayyukan da muka ga ana yi kuma an taso su a gaba babu dare babu rana insha’Allah za mu more su nan kusa, Naira za ta farfaɗo, ayyukan yi za su samu, tattalin arzikin Najeriya zai sake yin ƙarfi, babu yajin aikin makaratu da jami’o’i, babu na ma’aikata, za a ƙara albashi, Wallahi wallahi ban san wani ba, amma ni dai Rahma wannan ne ke riƙe da ni a gwamnati ba albashi ko alawus ko wata dama ba, na ga ana aikin farfaɗo da ƙasa ne nake so ni ma na samu ladar hakan. Wallahi ko yau na fahimci sabanin hakan tabbas, to ni mai haƙura da aikina ce na koma gwagwarmaya. Ban faɗi wannan don ku yarda ba sai don Allah Ya shaida. A yi haƙuri!!!

Rahama Abdulmajid manazarciya ce mai sharhi a kan al’amurra na yau da kullum musamman na siyasa. Kuma mataimakiya ta musamman ga shugaban ƙasa. Ta rubuto ne daga Birnin Tarayya Abuja.