Ma’aikata sun tsunduma yajin aiki a Neja
Daga BASHIR ISAH
Ma’aikatan gwamnati a Jihar Neja, sun fara yajin aikin sai-baba-ta-gani domin biyar haƙƙinsu a wajen gwamnati.
Da safiyar Laraba ma’aikatan suka fara yajin aikin bisa umarnin Ƙungiyar Ƙwadago (NLC) reahen jihar, lamarin da ya haifar da tsaiko a harkokin jihar.
NLC reshen jihar ta ɗauki wannan mataki ne bayan da gwamnatin jihar ta kasa cimma buƙatun mambobinta a jihar.
Shugaban NLC na jihar, Idrees Lafene da takwaransa na ƙungiyar ‘yan kasuwa, Ibrahim Gana, su ne suka bai wa ma’aikatan jihar unarnin shiga yakin aikin bisa abin da suka kira gazawa daga ɓangaren wamnati wajen kula da walwalar mambobinta.
Sakataren Gwamnatin Jihar, Abubakar Usman, ya shaida wa manema labarai a ranar Talata cewa, suna tattaunawa da shugabancin NLC domin daƙile yajin aikin.
Wannan shi ne karon farko da ma’aikatan jihar suka tsunduma yajin aiki a gwamnatin Mohammed Bago.
