Majalisar Wakilai ta gayyaci Akanta Janar na Ƙasa, Ogunjimi kan badaƙalar hukumar bogi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Akanta Janar na Ƙasa (AGF), Shamseldeen Ogunjimi zai gurfana a gaban kwamitin wucin-gadi na Majalisar Wakilai a yau Litinin domin amsa wasu tambayoyi akan badaƙalar hukumar bogi da ake kira da Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC).

Ogunjimi zai bayar ba’asi ne akan abin da ya sani game da yadda aka ware mata fiye da Naira biliyan 1.32 a cikin Kasafin Kuɗin shekarar 2026 duk da cewa babu ita.

Kwamitin, wanda ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Kanke/Kanam/Pankshin ta Jihar Filato, Yusuf Gagdi ke jagoranta, na gudanar da bincike ne akan yadda aka kafa PFIPC, wata hukuma da Gwamnatin Tarayya ta ce ba ta san da wanzuwarta ba.

Ana sa ran zaman zai mayar da hankali akan yadda aka sanya kuɗaɗen hukumar cikin kasafin kuɗi da kuma gano waɗanda ke da hannu a lamarin yayin ƙoƙarin gano haƙiƙanin al’amarin.

By Babaji

Leave a Reply