An kama sojan da ake nema kan sayarwa ‘yan ta’adda kayan sojoji yana ƙoƙarin tafiya Kamaru

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jami’an Rundunar Sojin Nijeriya sun yi nasarar kama jami’i Private Mohammed Yusuf, wanda a kwanan nan aka sanar ana neman sa ruwa a jallo bisa zargin sayar kayan inifom ɗin sojoji da wasu kayayyakinsu ga ‘yan ta’adda da sauran masu aikata miyagun laifuka.

Rahotanni sun bayyana cewa, an kama Yusuf ne da misalin ƙarfe 6:30 na yammacin ranar Asabar a matsayar motoci ta Jidar da ke Maiduguri a Jihar Borno, yayin da yake ƙoƙarin tafiya Jamhuriyar Kamaru.

Jami’in yaɗa labarai na sojojin Atisayen Haɗin Kai (OPHK) na riƙo, Kyaftin Mohammed Goni ne ya tabbatar da labarin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.

A cewar sojojin, an yi nasarar cafko jami’in ne yayin wani atisaye da dakarun rukuni na 7 na Provost suka ƙaddamar bisa wani bayani na sirri akan jami’in.

Goni ya bayyana cewa, an ayyana Private Yusuf mai lamba 23NA/84/1939 da ke a sashen sojoji na Ordnance Corps a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo ne a ranar 23 ga Yuli, 2026.

Bincike ya nuna cewa, jami’in ya ƙaurace wa zuwa aiki ne tun a ranar 7 ga Yuli, 2026, sannan ya koma Maiduguri, inda ya samu wata maɓoya a yankin Gomari Costain da ke Ƙaramar Hukumar Jere.

Kakakin sojojin ya bayyana cewa, wannan ya nuna yadda bayanan leƙen asiri ke taimaka wa ayyukansu dakarun tsaro da kuma ƙoƙarin rundunar wajen tunkarar ayyukan zangon-ƙasa acikin jami’anta.

Ya ƙara da cewa, tuni aka garzaya da jami’in komar hukumar, inda ake gudanar da bincike akansa domin gano haƙiƙanin al’amarin da kuma ƙoƙarin gano sauran waɗanda suke da hannu aciki.

By Babaji

Leave a Reply