
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Babachir Lawal, ya bayyana cewa marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙi tallata Shugaba Bola Ahmed Tinubu a filli a zaɓen 2023 ne saboda dalilan addini da lamuran ƙwarewa.
Babachir Lawal ya faɗi haka ne a wata hira da gidan talabijin na Symfoni a ranar Asabar, inda ya bayyana cewa da fari Buhari na ganin ba zai iya mara wa Tinubu baya ba a matsayin wanda zai gaje shi bisa la’akari da matsalolin lamuran addini da ƙwarewar siyasa.
A cewarsa, bayan tattaunawa da tsohon shugaban, Buhari ya amince da zama ɗan waje da barin deliget-deliget na APC a babban taronta na ƙasa su zaɓi wanda zai tsaya takarar Shugaban Ƙasa.
Tsohon sakataren gwamnatin Buharin ya kuma yaba wa gudunmawar da Tinubu ya bayar a lokutan yaƙin neman zaɓen APC, lamarin da ya sa ba zai nuna adawa da muradin Tinubu ba na zama shugaban ƙasa.
Ya ƙara da cewa, gabanin taron zaɓen fidda gwanin APC na ɗan takarar shugaban ƙasa, ya roƙi Buhari da ya guji nuna goyon baya ga kowane ɗan takara a fili, sannan a madadin haka ya bar ‘ya’yan jam’iyya su zaɓi wanda suke so jam’iyyar ta tsayar takara.
Hakan na zuwa yayin da al’umma a fagen siyasa ke ganin marigayin tsohon shugaban ƙasar a matsayin wanda bai shiga sahun masu goyon bayan Tinubu ba a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe duk da gudunmawar da ya bayar tun a lokacin kafa jam’iyyar da kuma nasarorin da ta riƙa samu daga 2015 zuwa yau.
