Daga JOHN D. WADA
a Lafia
Matar babban bishop na Iklisiyar Threshing Floor Watchman Assembly da ake kira Salvation City dake Bukan sidi a birnin Lafia jihar Nasarawa wato Rabaran Mary Ovye ta jaddada muhimmancin aiki tare tsakanin mabiya addinin Kirista don cimma manufa guda musamman samun rahamar ubangiji da kuma rai madauwami.
Rabaran Mary Ovye tayi kiran ne a lokacin da take wa’azin sujadar Iklisiyar ranar La’adi na mako da ake ciki a Iklisiyar.
Tace tabbas kiran ya zama wajibi idan aka yi la’akari da ɗimbin alfanu da kuma nasarori da ake samu a duk lokaci da mabiya Annabi Isa Almasihu suka haɗa kai suna aiki tare don cimma buri guda ta ayyuka dake ɗaukaka addinin kamar shelar bishara tare da gudanar da sujada tare da kai ziyarce-ziyarce da nuna so da ƙauna da sauran su waɗanda a cewar ta Ubangiji Allah na matuƙar so su yi hakan tare ako yaushe.
Tace bai kamata mabiya Isa Almasihu su rika ƙyashin junansu ba maimakon haka kowa yayi amfani da baiwa da Allah ya ba shi domin yin aiki tare don samun ɗimbin lada dake tattare da hakan daga ubangiji.
Rabaran Mary Ovye ta kuma bayyana cewa babu mabiyi da zai samu cigaba a rayuwarsa idan yana aiki shi kaɗai ba tare da ‘yan uwarsa ba, inda ta ƙalubalanci mambobin Iklisiyar su tabbatar suna kuma yin addu’a tare da sauran ibadodin don ta haka ne za su samu ruhi mai tsarki a rayuwarsu.
Ta kuma buƙace su su bi Allah da zuciyansu guda ba tare da gunaguni ba ko yin la’akari da kowa ba don a cewar ta hakan ne za su samu rai na har abada.
Har ila yau Rabaran Mary Ovye tayi amfani da damar inda ta alaƙanta rashin cigaba da samun nasara a rayuwar wasu mabiya Yesu Kirsti ga rashin canja tsalon rayuwarsu ta yau da kullum musamman ta gudanar da ibada da sauran su kana ta buƙace su su yi la’akari da hakan.
Ta ƙara da cewa rayuwa kan kasance cikin wahala da alhini a duk lokaci da mabiya su ka ƙi yin aiki tare musamman a fannin ibada kasancewar Allah ya bai wa kowa baiwa kuma so yake kowa yayi amfani da baiwar ta yadda yadace kuma a ranar gobe kiyama Allah zai tambayi kowa game da aiki da yayi da baiwar da ya ba shi.
Tun farkon wa’azin nata Rabaran Mary Ovye wacce ta karanto wasu sura da ayoyi daga littafi mai tsarki ta bibul da suka haɗa da Korantiyawa na farko sura 12 daga aya 14 da Zabura sura 133 aya 1 zuwa 3 da kuma Hebraniyawa sura 10 aya 25 inta ta jawo hankulan masu sujadar da sauran al’ummar Kirista baki ɗaya game da alfanu da ke tattare da yin aiki tare a kullum kana ta kammala wa’azin nata da yin wa mabiyan addu’a ta musamman don ƙarfafa imaninsu ga Allah da kuma ikon yin aiki tare a rayuwar su.
Wakilinmu a jihar ta Nasarawa John D. Wada ya kuma ruwaito cewa sauran ibadodin da aka gudanar a yayin sujadar Iklisiyar ta Lahadin sun hada da addu’oi da rera wakokin yabo da shedar godiya na musamman daga ƙungiyoyin Iklisiyar daban daban da sauran su.
