Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Cibiyar bunƙasa fasahar sadarwa da cigaban al’umma (CITAD) ta bayyana adawarta ga ƙudirin gyaran dokar kare bayanai ta Nijeriya ta 2023, wanda ke neman tilasta wa kamfanonin kafafen sada zumunta, masu sarrafa bayanai da masu kula da bayanai buɗe ofisoshi a cikin ƙasar. Cibiyar ta ce idan aka amince da kudirin, hakan na iya tauye haƙƙin dijital, rage ƙirƙire-ƙirƙire da kuma kawo cikas ga bunƙasar tattalin arzikin dijital na Nijeriya.
Da yake jawabi a taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar CITAD da ke Kano, daraktan zartarwa na cibiyar, Dakta Yunusa Zakari Ya’u, wanda jami’in kula da haƙƙokin dijital na CITAD, Ali Sabo, ya wakilta, ya bayyana cewa duk da kyakkyawar manufar ƙudirin da Sanata Ned Munir Nwoko ya gabatar, akwai yiwuwar ya haifar da matsalolin da ba a yi hasashe ba ga fannin fasaha a Nijeriya.
Ali Sabo ya ce CITAD tana goyon bayan duk wani ƙoƙari na ƙarfafa kariyar bayanai, inganta sa ido kan ayyukan kamfanonin dijital da tabbatar da ɗaukar alhaki. Sai dai ya ce tilasta wa dukkan dandamalin dijital su buɗe ofisoshi a Nijeriya zai ƙara musu nauyin doka da tsari tare da rage sha’awar masu zuba jari a fannin fasahar dijital.
Ya ƙara da cewa kudirin zai fi yin illa ga sabbin kamfanonin fasaha, ƙananan kamfanoni, ƙungiyoyin sa-kai, ayyukan buɗaɗɗen manhaja (Open Source) da sababbin dandamalin dijital, waɗanda ba su da ƙarfin kuɗin kafa da gudanar da ofisoshi a Nijeriya. A cewarsa, hakan kuma zai bai wa manyan kamfanonin fasaha na ƙasashen waje fifiko saboda ƙarfin kuɗinsu.
CITAD ta jaddada cewa dokar kare bayanai ta Nijeriya ta 2023 ta riga ta samar da cikakken tsarin doka na kare bayanan jama’a da kuma daidaita ayyukan ƙungiyoyin da ke sarrafa bayanan ‘yan Nijeriya. Saboda haka, cibiyar ta buƙaci ‘yan majalisa su mayar da hankali kan cikakken aiwatar da dokar da ake da ita maimakon ƙara sabbin sharuɗɗa.
Har ila yau, cibiyar ta yi watsi da ra’ayin cewa buɗe ofisoshi ne kaɗai hanyar tabbatar da ɗaukar alhaki. Ta ce ana iya gudanar da hulɗa da hukumomi, karɓar koke-koke, isar da sanarwar doka da kuma tabbatar da bin ƙa’idoji ta hanyar wakilan cikin gida da aka amince da su da kuma hanyoyin sadarwar dijital masu ingantaccen tsaro.
CITAD ta yi gargaɗin cewa ɗora wa kamfanonin dijital na ƙasashen waje nauyin doka fiye da kima na iya sa wasu daga cikinsu su rage ayyukansu ko kuma su fice gaba ɗaya daga kasuwar Nijeriya. Ta ce hakan zai yi mummunar illa ga miliyoyin matasa, ‘yan kasuwa, malamai, ƙungiyoyin farar hula da ƙananan sana’o’i da ke dogaro da kafafen dijital wajen sadarwa, ƙirƙire-ƙirƙire da gudanar da harkokin kasuwanci.
Don haka, CITAD ta buƙaci Majalisar Dokoki ta ƙasa ta dakatar da ci gaba da duba ƙudirin har sai an gudanar da cikakken tuntuba da ƙungiyoyin kare haƙƙin dijital, kamfanonin fasaha, ƙungiyoyin kare haƙƙin masu amfani da kayayyaki, masana kare bayanai, sabbin kamfanoni da sauran masu ruwa da tsaki.
Kazalika ta kuma ba da shawarar ƙarfafa hukumar kare bayanai ta Nijeriya, faɗaɗa haɗin gwiwa da hukumomin ƙasashen waje, naɗa wakilan cikin gida da aka amince da su da kuma amfani da matakan bin doka bisa tantance haɗari maimakon tilasta buɗe ofisoshi ga kowa.
Daga nan, CITAD ta jaddada cewa Nijeriya na buƙatar tsarin doka mai daidaito wanda zai kare sirrin jama’a tare da ƙarfafa ƙirƙire-ƙirƙire, bunƙasa amfani da fasahar dijital da haɓaka tattalin arziki.
Ta kuma yi kira ga Sanata Ned Munir Nwoko da sauran mambobin Majalisar Dokoki ta ƙasa da su sake nazarin ƙudirin tare da samar da manufofin da za su ƙarfafa ɗaukar wani mataki ba tare da tauye damar amfani da ayyukan dijital ko hana ci gaban fasaha ba.
