Dagà UMAR GARBA a Katsina
Mamakom ruwan kamar da bakin ƙwarya haɗe da iska ya rusa ɗaruruwan gidaje a garin Dangamau da ke ƙaramar hukumar Kusada ta jihar Katsina, al’umma a yankin sun rasa matsugunansu bayan wata guguwa mai ƙarfi haɗe da ruwan sama ta lalata gidaje, shaguna da sauran kadarori sama da 200, waɗanda darajarsu ta kai miliyoyin naira.
Wannan ibtila’i da ya faru a cikin makon da ya gabata ya sa iyalai da yawa sun rasa matsuguni da kuma kawo cikas ga harkokin tattalin arziki.
Da yake mayar da martani ga lamarin, Gwamnan jihar Katsina Dikko Raɗɗa ya nuna tausayawa ga mazauna yankin, yana mai bayyana ɓarnar a matsayin abin rashin jin daɗi.
Gwamnan ya ce asarar gidaje da kadarori masu daraja ya sanya iyalai da yawa cikin mawuyacin hali, kuma ya tabbatar wa waɗanda abin ya shafa cewa gwamnatin jihar za ta ba da tallafin da ake buƙata.
“A madadin gwamnati da mutanen jihar Katsina ina yi wa waɗanda wannan ibtila’i ya shafa ta’aziyya. Muna jin raɗaɗin da kuke ji kuma ba za mu bar ku ku kaɗai a wannan lokacin ba,” in ji Raɗɗa.
A matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin samar da taimako nan take, gwamnan ya umarci hukumomin gwamnati da abin ya shafa da su tantance girman ɓarnar da kuma fara ɗaukar matakan gaggawa.
Ya bayyana cewa an riga an fara shirye-shiryen kai kayan agaji da sauran nau’ikan tallafi ga gidajen da abin ya shafa.
“Ana kan gaba wajen samar da agaji ga mutanen da suka rasa matsugunansu. Za a samar da abinci, matsuguni da sauran buƙatu na yau da kullun ba tare da ɓata lokaci ba,” in ji shi.
Raɗɗa ya kuma buƙaci mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu su kuma haɗa kai da jami’an agajin gaggawa yayin da gwamnati ke ƙoƙarin dawo da zaman lafiya a cikin al’umma.
A cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan jihar, Ibrahim Kaula Mohammed, ya fitar a ranar Lahadi, gwamnan ya yi addu’ar Allah ya kare mazauna yankin daga irin wannan ibtila’i a faɗin jihar.
Wannan lamari ya ƙara yawan bala’o’in da suka shafi yanayi da aka samu a jihar Katsina a lokacin damina.
Mako guda kacal da ya gabata, a ranar 19 ga Yuli, ‘yan’uwa biyu – Muhammad Salisu mai shekaru 12 da Abdurrahman Salisu mai shekaru bakwai – sun rasa rayukansu a wani ambaliyar ruwa a yankin Janbango da ke cikin birnin Katsina.
An ruwaito cewa yaran suna dawowa daga wata makarantar Islamiyya da ke kusa lokacin da ruwan sama mai ƙarfi da guguwa ya cika hanyoyin ruwa har suka yi ambaliyya wanda ruwan ya tafi da su.
Bayan bincike mai zurfi da mazauna yankin suka yi, an samo gawarwakinsu daga wurare daban-daban, wanda hakan ya jefa al’umma cikin makoki.
Mahaifinsu, Malam Salisu Arabi, ya bayyana wannan ibtila’i a matsayin abin da ya fi raɗaɗi a rayuwarsa.
