Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Jami’an tsaro sun halaka ’yan bindiga sama da 40 da suka haɗa da manyan kwamandojin su da daƙile hari da ’yan bindigar suka kai a garin Guga da ke ƙaramar hukumar Bakori a Jihar.
Kwamishinan cikin gida da na jihar, Dr.Nasir Mu’azu, wanda ya fitar da sanarwar haka ya ce, sama da ’yan bindiga 200 ɗauke da makamai, ƙarƙashin jagorancin fitaccen shugaban ’yan bindiga Idi Abasu Aiki, tare da wasu ’yan ƙungiyar Ado Aleru, daga maƙwabciyar Jihar Zamfara, sun kai harin ramuwar gayya a garin Guga da misalin yammacin Lahadi.
Sai dai jami’an tsaro,bayan samun bayanan sirri suka ɗauki matakin gaggawa na fito na fito da ya tilasta wa ’yan bindigar ja da baya bayan sun yi asarar mutane sama da 40.
Sanarwar ta ce, jami’an sun tabbatar da kashe ƙusoshin manyan kwamandoji takwas, inda Idi Abasu Aiki ya samu munanan raunukan harbin bindiga.
Dr Danmusa, ya ce a halin yanzu jami’an tsaro sun fara aikin share yankin domin ƙwato makamai da sauran kayayyakin da ’yan bindigar suka bari, yayin da aka ƙara tsaurara sintiri da sa ido.
Sai dai gwamnatin jihar ta tabbatar da mutuwar mambobin ƙungiyar mafarauta su huɗu da suka gamu da ajalin su a lokacin da suke sayayya a wani shago a cikin garin Guga.
Gwamnatin Jihar Katsina ta miƙa sakon ta’aziya ga iyalan jami’an JTF da suka rasa rayukan su suna yaƙar ta’addanci .
Kwamishinan ya ce waɗannan jami’an tsaro na JTF sun sadaukar da rayukan su a yayin da suke ƙoƙarin kare yankin su wanda ba zai tafi a banza ba.
