Bashin kuɗin wutar lantarki: Tinubu ya bada umarin biyan bashin da ke kan Fadar Villa bayan AEDC ya yi barazanar katse wutar fadar

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bada umarni kan a biya bashin kuɗin wutar lantarkin da kamfanin Abuja Electricity Distribution Company (AEDC) ke bin Fadar Shugaban Ƙasa.

Wannan na zuwa ne biyo bayan sanarwar da AEDC ya fitar dangane da waɗanda yake bi bashin kuɗin wuta wanda ya haɗa da Fadar Villa da ke Abuja.

Da fari dai AEDC ya fitar da wata sanarwa inda ya yi barazanar katse wutar ma’aikatu da hukumomin gwamnati su 86, ciki har da Fadar Shugaban Ƙasa muddin suka ƙi biyan bashin kuɗin wautar lantarki biliyan N47.1 da ke kansu.

MANJAHA ta rawaito AEDC ya ce, “Hukumar Abuja Electricity Distribution Company (AEDC) ta bada wa’adin kwana 10 ga ma’aikatu da hukumomin gwamnati 86 kan su biya bashin kauɗin wuta, N47.1bn da ake bin su ko kuma su fuskanbci hatsarin yanke musu wuta.

“Bayan cikan wa’adin kwana 10 wanda zai ƙare ran Laraba, 28 ga Fabrairu, 2024, AEDC zai fara yanke wutar duk wanda bai biya bashin da ke kansa ba.”

Sauran wuraren da lamarin ya shafa sun haɗa da Barikin Babban Hafsan Tsaro, Ma’aikatar Birnin Tarayya, Ofishin Gwamnatin Jihar Neja da ke Abuja.

Sai kuma Ƙaramar Ma’aikatar Fetur, Fadar Shugaban Ƙasa, Ma’aikatar Ilimi, Babban Bankin Nijeriya, Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya da dai sauransu.

By Editor