Za a yanke wutar lantarki a Fadar Shugaban Ƙasa da CBN saboda bashi

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Kamfanin rarraba wutar lantarki, wato Abuja Electricity Distribution Company, ya ba da sanarwar zai yanke wutar lantarki a Fadar Shugaban Ƙasa da Babban Bankin Nijeriya (CBN) da wasu ma’aikatu da hukumomi 85 na Gwamnatin Tarayya saboda bashin kuɗin wuta da ya kai sama da Naira biliyan 47,195 ya zuwa Disamban 2023.

AEDC ya bayyana haka ne a cikin sanarwar da ya fitar a ranar Litinin, 19 ga Fabrairu, 2024.

AEDC ya bayyana cewa, “Hukumar Abuja Electricity Distribution Company (AEDC) ta bada wa’adin kwana 10 ga ma’aikatu da hukumomin gwamnati 86 kan su biya bashin kauɗin wuta, N47.1bn da ake bin su ko kuma su fuskanbci hatsarin yanke musu wuta.

“Bayan cikan wa’adin kwana 10 wanda zai ƙare ran Laraba, 28 ga Fabrairu, 2024, AEDC zai fara yanke wutar duk wanda bai biya bashin da ke kansa ba.”

Sauran wuraren da lamarin ya shafa sun haɗa da Barikin Babban Hafsan Tsaro, Ma’aikatar Birnin Tarayya, Ofishin Gwamnatin Jihar Neja da ke Abuja.

Sai kuma Ƙaramar Ma’aikatar Fetur, Fadar Shugaban Ƙasa, Ma’aikatar Ilimi, Babban Bankin Nijeriya, Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya da dai sauransu.

By Editor