Fadar Shugaban Ƙasa ta caccaki Atiku kan ɗaukar nauyin kamfanin Amurke don adawa da mulkin Tinubu

Spread the love

Fadar Shugaban Ƙasa ta caccaki tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, bayan zarginsa da ɗaukar hayar masu fafutukar siyasa a Amurka kan kuɗi dala miliyan 1.2 domin kai ƙorafi ga Shugaban Amurka, Donald Trump, da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka kan wata shari’ar ƙwace kadarori ta shekarar 1993 da ta shafi Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

A cikin wata sanarwa da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Alhamis, Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana matakin da ake zargin Atiku ya ɗauka a matsayin yunƙurin kai siyasar cikin gida zuwa ƙasashen waje tare da tauye martabar Najeriya a idon duniya.

Sanarwar mai taken “Yaushe Atiku Abubakar Zai Kai Kansa Gaban Shugaba Donald Trump?” ta ce burin Atiku na zama shugaban ƙasa ya sa ya manta da ɗabi’un dattaku da mutuncin da ake sa ran tsohon shugaban ƙasa ko babban ɗan siyasa ya nuna.

Fadar Shugaban Ƙasa ta ce abin mamaki ne yadda mutumin da ya shafe fiye da shekaru 30 yana neman shugabancin Najeriya zai kai ƙorafi kan shugaban ƙasarsa ga shugaban wata ƙasa.

Ta kuma jaddada cewa batun shari’ar ƙwace kadarorin da aka yi wa Shugaba Tinubu a Amurka an warware shi tun fiye da shekaru 30 da suka gabata, ba tare da samun wata hukuncin aikata laifi a kansa ba. A cewarta, al’ummar Najeriya sun riga sun yanke hukunci kan lamarin ta hanyar zaɓen 2023, sannan Kotun Ƙoli ta tabbatar da sakamakon zaɓen.

Fadar ta ƙara da cewa Najeriya ƙasa ce mai cikakken ’yanci, don haka kai ƙorafi kan shugaban ƙasa ga wata ƙasa ba wai kawai bai dace ba ne, har ma yana tauye martabar ƙasar.

A cikin sanarwar, Onanuga ya kuma buƙaci Atiku ya yi bayani kan tarihinsa na shari’o’i a Amurka, inda ya yi nuni da rahoton binciken Majalisar Dattawan Amurka na shekarar 2010 da kuma batun badakalar cin hanci da ta shafi tsohon ɗan Majalisar Wakilan Amurka, William Jefferson.

Sanarwar ta kuma zargi Atiku da gudanar da shirin sayar da kadarorin gwamnati lokacin da yake Mataimakin Shugaban Ƙasa, tana cewa an sayar da kadarorin ƙasa ga na kusa da gwamnati kan farashi mai rahusa, lamarin da ya haddasa asarar ayyukan yi da kuma matsalolin albashi da fansho.

A wani bangare mai ɗaukar hankali na sanarwar, Fadar Shugaban Ƙasa ta ce: “Da ace Atiku Abubakar ɗan ƙasar China ne, da tuni yana rubewa a gidan yari saboda laifukan da ya aikata kan al’ummar Najeriya.”

Har ila yau, sanarwar ta zargi Atiku da amfani da tsoffin zarge-zargen da aka tattauna tun lokacin yaƙin neman zaɓen 2023, tana mai cewa hakan ba zai ƙara masa damar lashe zaɓen 2027 ba.

A ƙarshe, Fadar Shugaban Ƙasa ta ce Shugaba Bola Tinubu bai damu da abin da ta kira “wasannin siyasa” na Atiku ba, domin yana mai da hankali ne kan aiwatar da manufofin Renewed Hope Agenda, da suka haɗa da farfaɗo da tattalin arziki, jawo hannun jari, inganta tsaro da kuma dawo da martabar Najeriya a idon duniya.

By Babaji

Leave a Reply