Gwamnatin Kano ta samar da gagarumin sauyi a asibitin Sheikh Muhammadu Jidda — Dakta Fatima Hamza

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Shugabar Asibitin ƙwararru na Sheikh Muhammadu Jidda, wanda aka fi sani da Asibitin Kura, Dakta Fatima Ibrahim Hamza, ta yabawa Gwamnatinjihar Kano bisa sauye-sauyen da ta ce an samu a asibitin, musamman a fannin samar da kayayyakin aiki da inganta ayyukan kiwon lafiya.

Dakta Fatima, wadda kuma ita ce Zonal Darakta na asibitin, ta bayyana hakan ne yayin da take zantawa da manema labarai a Kano.

Ta ce a cikin kusan shekaru biyu da ta shafe tana jagorantar asibitin, gwamnatinjihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ta aiwatar da muhimman ayyukan ci gaba da suka haɗa da samar da tsarin wutar lantarki mai amfani da hasken rana (solar) a sashen gaggawa (Emergency), dakin gwaje-gwaje (Laboratory), dakin haihuwa (Labour Room) da sauran muhimman sassan da ke amfani da na’urorin lantarki.

Ta ƙara da cewa gwamnati ta kuma samar da sabbin kayan aikin zamani a sashen ɗaukar jini da kuma sashen Physiotherapy, fannin da ta ƙware a kai.

A cewarta, lokacin da ta karɗi ragamar shugabancin asibitin, ɗaki guda ne kacal ake amfani da shi wajen gudanar da aikin Physiotherapy, amma yanzu an gina sabon sashe mai faɗi, kuma nan ba da daɗewa ba za a samar masa da cikakkun kayan aiki.

Dakta Fatima ta kuma bayyana cewa ana ci gaba da aikin gyaran asibitin gaba ɗaya, inda ta ce an kai kusan kashi 80 cikin 100 na kammala aikin.

Ta yabawa Hukumar KHETFUND ta Jihar Kano bisa gudunmawar da take bayarwa wajen bunƙasa ayyukan ci gaban asibitin.

Game da samar da magunguna, ta ce asibitin na ci gaba da samun ingantattun magunguna daga Hukumar Samar da Magunguna da Kayan Aikin Asibitoci ta Jihar Kano (DMCSA), inda ake sayar da su ga marasa lafiya cikin farashi mai sauƙi.

A ƙarshe, Dakta Fatima Ibrahim Hamza ta bayyana jin daɗinta da kyakkyawar alaƙar aiki da ke tsakaninta da ma’aikatan Asibitin ƙwararru na Sheikh Muhammadu Jidda, tana mai cewa haɗin kan da ake samu a tsakanin ma’aikata na taimakawa wajen inganta ayyukan kula da marasa lafiya.

By ukarofi

Leave a Reply