Al’ummar Gwazange sun koka kan rashin magudanan ruwa

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Al’ummar anguwar Gwazange da ke cikin garin Argungu sun koka bisa ga rashin magudanar ruwa a anguwar. Malam Mamuda Haruna, wani magidanci a madadin mutanen anguwar ya bayyana cewa rashin magudanar ruwa ya haifar da faɗuwar gine-ginen su wanda har ya yi sanadiyyar gidajen su sun cika da ruwa, hasali ma waɗansu a tsaye suka kwana da su da iyalan su.

Ya ƙara da cewa aƙalla sama da magidanta hamsin ke fuskantar barazanar rasa matsugunan su wanda idan abin ya zo da rashin sa’a ana iya rasa dukiyoyi da rayuka idan ba a ɗauki matakin gyara ba.
Ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa musamman ƴan siyasa zaɓaɓɓu da kuma gwamnati da su ɗauke nauyin da ya rataya a wuyan su na ceton rayuka da dukiyoyin su.
Sau da yawa idan aka yi ruwan sama musamman cikin dare mutanen anguwar sukan shiga damuwa da tashin hankali wanda a irin wannan yanayin ba kowa zai iya barin nasa gida ya je ya kaiwa maƙocin sa agaji ba.

By ukarofi

Leave a Reply