Majalisar Dattawa ta yi barazanar ladabtar da NNPCL, CBN, JAMB, NECO da sauran hukumomi kan ƙin amsa gayyatarta

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Majalisar Dattawan Nijeriya ta yi barazanar amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya ba ta wajen ɗaukar mataki a kan wasu Ma’aikatu, Hukumomi da Cibiyoyin Gwamnati (MDAs) da suka ƙi amsa gayyatar Kwamitinta kan Harkokin Kuɗi domin gudanar da binciken sa ido.

Barazanar ta fito ne bayan shugaban kwamitin, Sanata Sani Musa (Niger ta Gabas), ya gabatar da batu a zaman majalisar na ranar Laraba.

Sanata Musa ya ce kwamitin na gudanar da bincike lokaci-lokaci bisa tanadin sashe na 88 da 89 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya domin tantance yadda hukumomin gwamnati ke tafiyar da kuɗaɗensu.

Ya ce binciken ya haɗa da duba kuɗaɗen shiga da hukumomin ke samu da kansu, harajin tambari (Stamp Duties), ribar gudanarwa, kuɗaɗen da ya kamata a tura Asusun Haɗaɗɗen Kuɗaɗen Shiga na ƙasa (Consolidated Reɓenue Fund), da kuma tabbatar da bin dokokin kuɗi na ƙasa.

Sai dai ya nuna damuwa cewa duk da gayyatar da aka aika wa hukumomin bisa ƙa’ida, wasu sun ƙi halarta, yayin da wasu kuma suka yi iƙirarin cewa ba su da wani wajibcin bayyana a gaban kwamitin ko miƙa bayanan da aka nema.

A cewarsa, irin wannan mataki barazana ce ga ikon Majalisar Dokoki na gudanar da aikin sa ido, kuma zai iya raunana gaskiya, riƙon amana da kuma tabbatar da amfani da dukiyar al’umma yadda ya kamata.

Sanatan ya kuma zargi wasu hukumomin da ke tara kuɗaɗen shiga da karya Dokar Fiscal Responsibility Act da kuma Finance Act 2022, ta hanyar riƙe mafi yawan kuɗaɗen shiga tare da mayar wa gwamnati kaɗan daga ciki.

Hukumomin da ya ce sun ƙi amsa gayyatar kwamitin sun haɗa da Kamfanin Man Fetur na ƙasa (NNPCL), Asusun Tallafa wa Manyan Makarantu (TETFund), Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Nijeriya (FAAN), Hukumar Kula da Sufurinjiragen Sama (NCAA), Hukumar Kula da Harkokin Ruwa da Tsaron Teku (NIMASA), Hukumar Bunƙasa ƙanana da Matsakaitan Masana’antu (SMEDAN), Hukumar Kula da Ingancin Kayayyaki (SON), Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON), Ofishin Akanta Janar na Tarayya, Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na ƙasa (TCN), Babban Bankin Nijeriya (CBN), Bankin NEɗIM, Hukumar Bunƙasa Fitar da Kaya (NEPC), Hukumar Masu Jiragen Ruwa ta Nijeriya, Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a (JAMB), Hukumar Shirya Jarabawar Kammala Makaranta (NECO), Hukumar Inshorar Ajiyar Kuɗi (NDIC), Gidan Rediyon Tarayya (FRCN), Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Jabi, da sauran wasu hukumomi.

A nasa jawabin, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya sake jaddada cewa Kundin Tsarin Mulki ya bai wa Majalisar cikakken ikon tilasta wa jami’an gwamnati da hukumomi bayyana a gabanta idan an gayyace su.

Ya yi watsi da ikirarin da wasu hukumomi ke yi cewa kwamitocin Majalisar ba su da ikon gayyatarsu, tare da umartar Sanata Sani Musa ya gabatar da cikakkiyar kudiri domin a tilasta shugabannin hukumomin da suka ƙi amsa gayyata su bayyana a gaban kwamitin.

“Ka kawo cikakkiyar kudiri. ɗaya daga cikin buƙatunta shi ne a tilasta musu bayyana a gaban Majalisar ƙasa ta hannun kwamitinka,” inji Akpabio.

Ya ƙara da cewa Majalisar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ɗaukar matakin da ya dace idan hukumomin suka ci gaba da yin watsi da gayyatarta.

“Idan har suka ƙi bayyana a ƙarshe, mun san matakin da ya dace mu ɗauka,” inji shi.

By ukarofi

Leave a Reply