Yadda gwamnatin Nijeriya ta kashe farfagandar gallaza wa Kiristoci

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Bayanan da ke cikin manhajar Gwamnatin Tarayya mai bibiyar kashe kuɗaɗen gwamnati (wato GovSpend) sun nuna cewa, Gwamnatin Nijeriya a ƙarƙashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu ta kashe Naira miliyan 500 a shekarar 2025, domin gudanar da wani shiri na gaggawa na yaɗa saƙon gwamnati a cikin gida da ƙasashen waje kan yadda ake ɓata sunan ƙasar a idanun Gwamnatin Amurka ta fuskar zaregin muzguna wa Kiristoci a cikin Nijeriya.

An bayyana cewa, manufar shirin ita ce mayar da martani ga abin da gwamnatin ta kira ‘yaɗa farfaganda daga ƙasashen Yamma’ da ke zargin ana gallaza wa Kiristoci a Nijeriya. Bayanan sun nuna cewa an ware kuɗin ne domin Ofishin Mai Bai wa Shugaban ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai da Sadarwa kan Manufofi, inda aka bayyana manufar kuɗin da cewa za a yi amfani da su wajen gudanar da yaƙin yaɗa bayanai da hulɗa da kafafen yaɗa labarai na duniya domin ƙalubalantar waɗannan zarge-zarge. An biya kuɗin ne a ranar 19 ga Disamba, 2025.

Rahoton ya kuma bayyana cewa a wannan shekarar ne Gwamnatin Tarayya ta ɗauki wani kamfanin hulɗa da masu yanke hukunci da yaɗa manufofi na Amurka, DCI Group, a ƙarƙashin kwangilar da ta kai dala miliyan tara. Takardun da aka shigar ƙarƙashin Dokar Rijistar Wakilan ƙasashen Waje ta Amurka (FARA) sun nuna cewa Aster Legal, wani kamfanin lauyoyi da ke Kaduna, ne ya ɗauki DCI Group a madadin Mai Bai wa Shugaban Ƙƙaa Shawara kan Harkokin Tsaro (NSA), Nuhu Ribadu.

Yarjejeniyar da aka sanya wa hannu a ranar 18 ga Disamba, 2025, ta tanadi cewa kamfanin zai taimaka wajen bayyana wa jami’an gwamnatin Amurka irin matakan da Nijeriya ke ɗauka na kare al’ummomin Kiristoci, tare da tabbatar da ci gaba da samun goyon bayan Amurka a yaƙin da ake yi da ƙungiyoyin ta’addanci a Yammacin Afirka.

A ƙarƙashin yarjejeniyar, gwamnatin Nijeriya ta amince da biyan kamfanin dala 750,000 duk wata, wanda zai kai dala miliyan tara cikin shekara guda idan aka ci gaba da yarjejeniyar. Rahoton ya ce, wannan mataki ya biyo bayan ƙarin matsin lamba daga wasu ‘yan siyasar Amurka dangane da rahotannin hare-haren da ke shafar al’ummomin Kiristoci a Nijeriya.

A watan Oktoban 2025, Shugaban Amurka Donald Trump ya sake sanya Nijeriya cikin jerin ƙasashen da ake wa laƙƙbi da “ƙasashe Masu Damuwa (CPC)”, bisa zargin take ‘yancin addini, musamman kan batun hare-haren da ake zargin suna shafar Kiristoci.

Wannan matsayi na CPC na daga cikin manyan matakan da gwamnatin Amurka ke ɗauka kan ƙasashen da ake zargi da take ‘yancin addini, kuma yana iya haifar da takunkumi ko wasu matakan diflomasiyya, sai dai shugaban ƙasar na da ikon dakatar da aiwatar da irin waɗannan matakai idan hakan ya dace da muradun tsaro ko manufofin ƙasarsa. Duk da wannan mataki, rahoton ya nuna cewa haɗin gwiwar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka ya ci gaba.

Amurka na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan abokan hulɗar Nijeriya wajen yaƙi da Boko Haram, ISWAP da sauran ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi, ta hanyar musayar bayanan sirri, horas da sojoji, sayar da kayan yaƙi, tallafin dabarun tsaro da kuma ayyukan jin ƙai.

A kwanakin baya gwamnatin Nijeriya ta fitar da wasiƙar da ta ce Donald Trump ya aikawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda shugaban Amurkan ya yaba da ƙoƙarin gwamnatin Nijeriya wajen yaƙi da ta’addanci, tare da amincewa cewa hare-haren da ke shafar al’ummomin Kiristoci na daga cikin matsalolin da ƙasar ke fuskanta.

Gwamnatin Tarayya ta ci gaba da jaddada cewa matsalar tsaro a Nijeriya ba ta samo asali daga wata manufa ta gallaza wa mabiyan wani addini ba. A cewarta, ta’addanci, ‘yan bindiga, rikice-rikicen ƙabilanci da sauran ayyukan laifi ne ke haddasa rikicin, kuma Kiristoci da Musulmi duk suna cikin waɗanda abin ya shafa. Rahoton ya ce, bayanan GovSpend da kwangilar kamfanin DCI Group sun nuna cewa gwamnatin Nijeriya ta ɗauki dabarun yaɗa saƙo a cikin gida da kuma ƙasashen waje domin kare martabarta kan batun zargin gallaza wa Kiristoci.

A cewar bayanan ACLED, Nijeriya ta fuskanci rikice-rikice 7,956 tsakanin Yulin 2025 da Yunin 2026, lamarin da ya yi sanadin mutuwar kusan mutum 15,000, yayin da aka kiyasta cewa mutane miliyan 66.8 sun kasance cikin haɗarin tashe-tashen hankula da rashin tsaro. Bayanan sun nuna cewa ana samun matsakaicin rikice-rikice 663 a kowane wata, 126 a mako, da fiye da 21 a kowace rana.

Haka kuma ana samun matsakaicin mutuwar mutum 1,237 a wata, 285 a mako, da kusan 41 a rana. Rahoton ya kuma nuna cewa Nijeriya ta ɗauki kaso 6.11 cikin ɗari na dukkan mutanen da suka mutu sakamakon rikice-rikice a duniya cikin wannan lokaci.

Jihar Borno ce ta zo ta farko da rikici 1,218, sai Katsina (958), Zamfara (885), Sakkwato (599), Kaduna (390), Benuwe (377) da Filato (346). Rahoton ya bayyana cewa waɗannan alƙaluma sun haɗa da hare-haren masu tayar da ƙayar baya, ‘yan bindiga, rikicin makiyaya da manoma, rikice-rikicen al’umma, hare-haren masu neman ɓallewa da kuma garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa. Duk da haka, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sha nanata cewa gwamnatinsa za ta kawo ƙarshen ta’addanci da ‘yan bindiga.

Yayin da wasu ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam na ƙasa da ƙasa ke cewa Kiristoci sun fi fuskantar hare-hare a wasu yankunan Nijeriya, gwamnatin tarayya ta dage cewa babu wata manufa ta gwamnati ta gallaza wa mabiyan wani addini, tana mai cewa Musulmi da Kiristoci duk suna cikin waɗanda rikice-rikicen ke shafa, kuma jami’an tsaro na kai farmaki ne ga masu aikata laifi ba tare da la’akari da addininsu ba.

Har ila yau, rahoton ya nuna cewa ba gwamnatin tarayya kaɗai ba ce ke ɗaukar kamfanonin hulɗa da masu yanke hukunci a ƙasashen waje, domin jihohi da cibiyoyin gwamnati da dama sun taɓa yin hakan domin bunƙasa zuba jari, inganta hulɗar diflomasiyya da kare martabar Nijeriya.

Rahoton ya ƙara da cewa, ƙungiyoyi masu alaƙa da Haramtacciyar ƙungiyar IPOB da masu fafutukar ƙasar Biyafara sun taɓa ɗaukar irin waɗannan kamfanoni a Amurka domin yaɗa manufofinsu da neman goyon bayan ƙasa da ƙasa.

By ukarofi

Leave a Reply