Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Wasu iyalai a Jihar Zamfara na roƙon hukumar kare haƙƙin ɗan Adam ta ƙasa da ƙungiyoyin lauyoyi da su shiga lamarin bayan wata malama mai shekara 28, Zainab Abdullahi, ta rasu sakamakon zargin sojoji sun kashe ta a kan hanyarta ta zuwa aiki a Gusau a ranar Talata da ta gabata.
Zainab, wacce ke koyarwa a wata makarantar mata a babban birnin jihar, ta rasu ne bayan shaidu sun ce wata motar soja ta buge babur din da ta hau sannan suka tsere. An yi jana’izar ta a ranar da ta mutu bisa ga koyarwar Musulunci.
Ɗan uwanta, Aliyu Abdullahi, ya shaida wa jaridar Blueprint Manhaja cewa lamarin ya bar iyalan cikin baƙin ciki, musamman ma da aurenta na kusa da wata ɗaya tilo.
“Wannan abin da aka yi zalunci ne,” in ji Aliyu. “ tana kan hanyar zuwa aikin ta na malanta. Wata ɗaya da wasu ’yan kwanaki suka rage a aurenta. Wannan ya jefa iyalanmu da abokanmu cikin baƙin ciki mai yawa.”
A cewar Aliyu, shaidun da suka ga abin sun shaida masu cewa sojoji ne da ke cikin mota suka buɗe ƙofa suka buge babur din da Hadiza ke kai, sannan suka gudu.
“Abin da shaidu suka faɗa mana shi ne sojoji sun buɗe ƙofar motar su suka buge babur din da take a kai, sannan suka tsere. Lamarin ya sa ta fada cikin magunar ruwa kuma ta mutu nan take,” in ji shi.
Aliyu ya ce ba su da karfin kuɗi da za su gurfanar da ƙarar a kotu don haka su na roƙon taimako.
Yana roƙon cibiyoyi biyu da su shiga lamarin: Hukumar ƙare haƙƙin ɗan Adam ta ƙasa da kuma ƙungiyar lauyoyin musulmi, reshen Jihar Zamfara.
“Muna roƙon rundunar soji ta Jihar Zamfara da gwamnatin jihar da su gano waɗanda suka aikata wannan kisan domin a hukunta su,” in ji Aliyu.
Ya buƙaci hukumomin soji da su gudanar da bincike cikin gaskiya su kuma gurfanar da masu laifin.
Har zuwa lokacin da aka haɗa wannan rahoton, rundunar soji ta Gusau ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba kan wannan zargi.
