Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
An fara sayar da takin zamani na mai sauƙin farashi na gwamnatin Jihar Gombe a ƙaramar hukumar Shongom, inda ake sayar da kowanne buhu kan farashin Naira 32,000 domin tallafa wa manoma da kuma bunƙasa samar da abinci.
Da yake ƙaddamar da shirin, shugaban ƙaramar hukumar Shongom, Modi D. Shelpidi, ya ce gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ta samar da tallafin ne domin rage wa manoma raɗaɗin tsadar taki tare da ƙara yawan amfanin gona a wannan kakar noma.
Ya buƙaci manoma su yi amfani da damar wajen sayen takin, yana mai jaddada cewa za a gudanar da rabon cikin gaskiya da adalci domin tabbatar da cewa manoma na haƙiƙa ne suka ci gajiyar shirin.
Shelpidi ya yaba wa gwamnatin jihar kan ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen tallafa wa ɓangaren noma, yana mai cewa noma shi ne ginshiƙin tattalin arzikin mafi yawan al’ummar Shongom, don haka ƙaramar hukumar za ta ci gaba da mara wa irin waɗannan tsare-tsare baya.
Wasu daga cikin manoman da suka amfana sun bayyana jin daɗin su kan sayar da takin a farashi mai sauƙi.
Malam Adamu Usman daga Filiya ya ce matakin zai taimaka wa ƙananan manoma su ƙara faɗaɗa ayyukansu na noma, yayin da Hajiya Amina Ibrahim daga Boh ta bayyana cewa tallafin ya zo a daidai lokacin da tsadar taki ke barazana ga noman bana.
Shi ma Malam Musa Sale daga Burak ya yaba wa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya da shugaban ƙaramar hukumar Shongom bisa tabbatar da cewa takin ya isa ga manoman da suka cancanta, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen ƙara yawan amfanin gona da inganta wadatar abinci a jihar.
