
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar ’Yan Sanda a Jihar Jigawa, ta ce ta fara gudanar da bincike akan mutuwar wani tsohon ɗan kimanin shekaru 60 da ya rasu bayan shiga halin kulawar gaggawa a wani ɗakin otel da ke Dutse, babban birnin jihar.
Al’amarin ya auku ne a ranar Talata, 21 ga Yuli, 2026, yayin da ya je otel ɗin da wata mata mai shekaru 20.
A wata sanarwa da jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, SP Lawan Shiisu Adam ya fitar, ya ce marigayin ya shiga otal ɗin tare da wata mata mai shekara 20.
A cewarsa, mutumin ya fara fama da matsalar numfashi ne bayan ya nemi a kawo masa abinci.
Sanarwar ta ce, akan haka ne aka garzaya da shi Babban Asibitin Dutse, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.
Rundunar ta bayyana cewa an samu wasu nau’ikan abinci, abubuwan sha, kayayyakin marigayin da kuma wani sinadari da ake zargin na ƙara ƙarfin maza ne a cikin ɗakin otal ɗin.
‘Yan sanda sun ce an miƙa gawar mamacin ga iyalansa domin gudanar da jana’iza, yayin da matar da ta kasance tare da shi ke cigaba da ba wa jami’an bincike ba’asin akan al’amarin.
Kazalika, rundunar ta buƙaci al’umma da su guji yaɗa jita-jita ko bayanan da ba a tabbatar da su ba, tana mai jaddada cewa bincike kan lamarin na cigaba da gudana.
A watan Junairun 2025 ne aka samu makamancin irin wannan labari, inda wani sufeton ‘yan sanda ya rasu a otel a Jihar Jigawa bayan shiga halin neman agajin gaggawa.
A yayin binciken ‘yan sanda, an gano wasu magunguna da sinadarai da aka alaƙanta su da na ƙara ƙarfin maza.
