Burin kowanne marubuci ne ya rubuta labari, ya ga ya koma fim – Jibrin Kaila 

Spread the love

“Kiyaye ƙa’idojin rubutu shi ne ƙashin bayan kowanne rubutu”

(Ci gaba daga mako mai zuwa)

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

Sunan Jibrin Yusuf Kaila ba ɓoyayyen suna ba ne, musamman ga marubuta masu mu’amala da kafafen sada zumunta. Matashi ne mai tsananin shauƙin son karance-karance da rubuce-rubuce. Yana kuma yawan rubutu kan tambihi game da harkokin rubutu da ƙalubalen marubuta. Ya fito ne daga ƙaramar Hukumar Haɗejiya ta Jihar Jigawa. A wannan makon wakilin Blueprint Manhaja Abba Abubakar Yakubu ya tattauna da shi game da gudunmawar sa a harkar adabi da kuma shawarwarinsa ga matasan marubuta ýan’uwan sa. A yi karatu lafiya.

MANHAJA: Akwai da dama marubutan Hausa da yanzu sun koma harkar rubutun fim, sun jingine labarin zube, kana ganin me ya kawo haka?

JIBRIN KAILA: E, gaskiya ne ana samun haka sosai, dalilin hakan kuwa ba ya rasa nasaba da yadda harkar rubutun fim ta fi kawo kuɗi. Don sai ka buga littafin guda 500 amma riba ba ta kai ta kawo ba, shi kuwa fim a fim a series ɗaya sai ka ninka ribar littafin da ka buga sau biyu, musamman idan an dace mai ɗaukar nauyin fim ɗin yana kyakykyawar sallama. Amma ko a marubutan ba kowa ne yake da hanyar shiga rubutun fim ba, akwai da dama da basu da ubangidan da zai shige musu gaba don samu wannan damar. Burin kowanne marubuci ne ya rubuta labari, kuma ya ga ya koma fim.

A ganinka wacce hanya ya dace matasan marubuta su fito da shi don bunƙasa kasuwancin littattafan da suke rubutawa?

Akwai hanyoyin da yawa musamman yadda muke cikin wani zamani mai sauƙi ga wanda ya karɓa, saboda zamani ba ƙarya ba ne, tun da Allah Ya yi rantsuwa a kansa. 

Abin ya dace shi ne su rungumi dabarun tallata littattafan su a hanyar zamani, domin jan hankalin masu karatu. Sannan su riƙa rubuta ingantaccen littafi mai jan hankali, kuma su yi amfani da kafafen sada zumunta wajen yaɗa labaran nasu, da ɗan taƙaitaccen bayani, sharhi, ko karanta wani ɓangare domin jan hankalin masu karatu. Haka kuma, su riƙa halartar tarukan bajekolin littattafai, tarukan marubuta, da shirye-shiryen makarantu domin gabatar da ayyukansu kai tsaye. Yin haɗin gwiwa da sauran marubuta, masu nazari, da masu tasiri a kafafen sada zumunta zai ƙara faɗaɗa kasuwancin su. Amfani da bidiyo wajen yin gajerun bidiyoyi da ke gabatar da littafi ko jigon labari a kafafen sada zumunta, hakan zai kwaɗaitar da masu karatu. Sai kuma amfani da salon kasuwancin littattafai ta hanyar manhajojin sayar da littafi a yanar gizo, kamar irin su Arewapen, Bakandamiya da su Amzon.

Har yanzu manazarta na nuna damuwa kan yadda akasarin marubutan Hausa na yanzu ba sa kiyaye ƙa’idojin rubutu, don haka rubutun nasu ba ya tasiri, zuwa inda ya kamata ya kai. Kai mene ne tunaninka akan haka?

Haƙiƙa kiyaye ƙa’idojin rubutu shi ne ƙashin bayan kowanne rubutu, don shi zai fito da ma’anar rubutu, rashin kyan rubutu yana sa da zarar ka bai wa wani ya karanta sai ya ga rubutun ya canja ma’anar sa. Wannan duk saboda rashin bin ƙa’idojin rubutu ne. A fahimtata saƙon marubuci ba ya kammala sai ya bi ƙa’idojin rubutu. Lallai akwai buƙatar kowanne marubuci ya samu wani na kusa da shi, wanda ya san ƙa’idojin rubutu yana gyara masa, don ilimi kogi ne.

Bayan ƙoƙarin da ka ke yi na yaɗa ayyukan wasu marubutan, shin kana samun damar karatun littafi, kuma a halin yanzu wanne littafin ka ke karantawa?

Tabbas ina samun karanta wasu littattafin, don ƙa’ida ce ta kowani marubuci ya kasance mai karance-karance, domin shi ne zai bashi damar sanin hanyoyi da dabarun rubuta labari da sanin ƙa’idojin rubutu. Littafin da nake kan karantawa yanzu shi ne ‘Ruwa da Wuta’ na marubuciya Amrah Auwal Mashi, Gwarzowar Gasar Hikayata ta BBC Hausa a 2024.

Wacce shawara ka ke da ita ga sauran marubuta ýan’uwan ka?

Marubuci ya kamata ya fahimci cewa alƙalaminsa ba kawai yana rubuta labari ba ne don nishaɗi.Ya sani ginshiƙan tarihinsa da abin da zai bar wa duniya bayan rayuwarsa akwai rubutu. Saboda haka, yana da muhimmanci ya riƙa tsaftace rubutunsa. Rubutu mai kyau ba ya tsufa, kuma ba ya gushewa tare da wanda ya rubuta shi. Akwai marubuta da dama da suka rasu shekaru masu yawa da suka wuce, amma har yau ana karanta littattafansu, ana nazarinsu, ana koyar da su a makarantu, kuma ana ambaton sunayensu cikin girmamawa saboda kyawawan abin da suka bari. Wannan shi ya sa nake yawan cewa, marubuci ba ya mutuwa; rubutunsa ne ke ci gaba da rayuwa, yana wakiltarsa a cikin al’umma. 

Idan aka adana waɗannan rubuce-rubuce cikin tsari, za su zama abin bincike ga masu nazari, abin koyi ga sabbin marubuta, da kuma gadon ilimi ga al’umma.

Haka kuma, ‘ya’yan da za su bari a baya za su yi alfahari da cewa iyayensu sun rayu da abin alheri, sun yi wa jama’a hidima ta hanyar ilimi da adabi. Ba wai sun bar dukiya kaɗai ba, sun bar tarihin da ake karantawa, ana yabawa, kuma ana yi musu addu’a saboda irin gudunmawar da suka bayar. Wannan ita ce mafi girman nasarar marubuci: ya rayu da mutunci, ya rubuta da gaskiya, ya bar abin amfani, kuma sunansa ya ci gaba da haskakawa a zukatan mutane ko bayan ya bar duniya. Haka nima nake fata a duniyar rubutu bayan na mutu.

To, madalla. Muna godiya.

Ina godiya matuƙa. Allah Ya saka da alheri.

By ukarofi

Leave a Reply