
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙwarya-ƙwaryar kwamitin Majalisar Wakilai kan binciken badaƙalar hukumar bogi ta PFIPC, ya koka kan yadda jagororin wasu ma’aikatu da hukumomi suka ƙi amsa gayyatarsa akan al’amarin.
A ranar Talata bayan kammala zaman majalisar ne shugabancin kwamitin ya bayyana wannan koke, inda ya ce rashin amsa gayyatar tasu na haifar da koma-baya ga aikin binciken da suke gudanarwa da kuma matakin shari’a akan hukumar.
Haka kuma, kwamitin ya soki rashin ganin Ministan Kuɗi, Taiwo Oyedele, wanda wani jami’in ma’aikatar ya wakilce shi, yana mai cewa wajibi ne su amsa gayyatar kai-tsaye na zuwa da kansu ko su fuskanci ɗaukar mataki daga majalisa.
A cewar Shugaban kwamitin, Yusuf Gagdi, kwamitin ba zai lamunci rashin biyayya ga umarninsa ba, inda ya ce suna buƙatar a ba su cikakken haɗin kai daga mutane da dukkan cibiyoyin da ke da alaƙa da binciken.
Baya ga haka, kwamitin ya kuma gayyaci Ministar Harkokin Waje, Misis Bianca Odumegwu-Ojukwu da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkar Tsaro, Nuhu Ribaɗu domin su yi bayanin yadda aka yi Hukumar Ci-gaban Harkokin Zuba Jari a ƙasashen waje ta Shugaban Ƙasa (PFIPC), ke gudanar da harkokinta duk da cewa akwai alamar tambaya akan halascinta.
