
Tsohon fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Faransa, Zinedine Zidane, ya rattaba hannu kan yarjejeniya da za ta ba shi damar zama sabon kocin tawagar ƙasar Faransa har zuwa watan Yunin 2030, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Kwararren ɗan jaridar kasuwar musayar ‘yan wasa, Fabrizio Romano, ne ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook, inda ya ce za a gabatar da Zidane a hukumance cikin kwanaki masu zuwa.
Rahoton ya ce Zidane zai jagoranci Faransa a gasar UEFA Nations League ta 2027, Gasar Kofin Nahiyar Turai (Euro 2028), da kuma Gasar Cin Kofin Duniya ta 2030.
Zidane mai shekaru 54 bai riƙe aikin horarwa ba tun bayan da ya bar Real Madrid a shekarar 2021. A lokacin da yake jagorantar ƙungiyar, ya lashe kofin UEFA Champions League sau uku a jere tsakanin 2016 da 2018, tare da kofin La Liga sau biyu da wasu manyan kofuna.
An daɗe ana alaƙanta Zidane da aikin horar da tawagar Faransa, inda ake sa ran zai gaji Didier Deschamps bayan kammala Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026.
Sai dai, har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Faransa ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance da ke tabbatar da naɗin Zidane ba.
