‘Yan bindiga sun kashe manoma biyu a sabon harin Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

‘Yan bindiga masu ɗauke da makamai sun kashe manoma biyu da safiyar yau Talata bayan sun kai hari garin Faru da ke ƙaramar hukumar Maradun ta Jihar Zamfara.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa wakilinmu cewa maharan sun kutsa garin da sassafe yayin da manoma ke shirin zuwa gonakinsu sannan suka fara harbe-harbe a sama.

“Sun kewaye garin da safe yayin da manoma ke zuwa gonakinsu suka fara harbi a sama,” mazaunin ya ce.

Mutane biyu da aka kashe a harin. Mazaunin yankin ya bayyana waɗanda aka kashe da suna Basharu Hakimi Yarbangi da Malam Samaila Faru.

Mazaunin ya bayyana halin da yankin ke ciki a matsayin mai tsanani, yana mai cewa hare-hare sun zama kusan kowace rana.

“Muna cikin mawuyacin hali domin ‘yan bindiga suna kai wa yankinmu hari kusan kowace rana,” in ji shi.

A cewarsa, al’ummomi da dama a ƙaramar hukumar Maradun a halin yanzu suna ƙarƙashin ikon ‘yan bindiga da ke da sansani a dajin Bayan Ruwa.

Ya lissafa garuruwan da lamarin ya shafa da suka haɗa da: Magamin Diddi, Kaya, Janbako, Gidan Goga, da Faru.

“Muna buƙatar ƙarin jami’an tsaro a yankinmu domin magance ‘yan ta’addan da ke addabar yankinmu,” ya roka.

Mazaunin ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Zamfara da Gwamnatin Tarayya da su gaggauta tura ƙarin jami’an tsaro yankin domin mayar da zaman lafiya da kare al’ummar yankin.

Jihar Zamfara na ci gaba da fama da matsalar ‘yan bindiga da sace-sace, musamman a ƙananan hukumomin karkara da ke kan iyakar dazuka da ke zama mafaka ga ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai.

Al’ummomin manoma a Maradun, Anka, da Bukkuyum sun daɗe suna kai rahoton hare-hare da suka rushe harkokin noma tare da yin ƙaura da mazauna yankin.

Ƙoƙarin tuntubar rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara domin jin ta bakinsu bai yi nasara ba har zuwa lokacin da ake haɗa wannan rahoton.

By ukarofi