Tarihin Muhammadu Kanta, wanda ya assasa Daular Kabi (I)

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Muhammadu Kanta na daga cikin fitattun jaruman da suka taka muhimmiyar rawa a tarihin Arewacin Nijeriya da yankin Yammacin Afirka. Shi ne ya assasa Daular Kabi, wadda ta zama ɗaya daga cikin manyan daulolin Hausa kafin zuwan Turawan mulkin mallaka. Har zuwa yau, zuriyarsa ce ke ci gaba da riƙe sarautar Kabi mai hedikwata a Argungu, Jihar Kebbi.

Asalinsa:

Riwayoyi sun nuna cewa Muhammadu Kanta ya fito ne daga zuriyar Usman ɗan Mas’ud, wanda ake cewa yana cikin mutanen da suke hidima a Haramin Ka’aba tun kafin bayyanar addinin Musulunci.

Bayan Musulunci ya bunƙasa, kakanninsa sun yi hijira daga Makka zuwa ƙasar Hausa domin yaɗa addini da kuma kasuwanci. Daga ƙarshe suka zauna a wani wuri da ake kira Kuyanbana, a yankin Katsina, inda zuriyarsu ta ci gaba da bunƙasa har aka haifi Muhammadu Kanta.

An ce sunan mahaifinsa Makata, yayin da mahaifiyarsa ake kira Tamatu. Dukkansu sun fito ne daga dangin Lekawa.

Jarumtarsa tun yana ƙarami:

Tun yana ƙaramin yaro, Muhammadu Kanta ya yi fice wajen ƙarfin hali da jaruntaka. Saboda irin bajintar da yake nunawa a kokawa, dambe da sauran wasannin mazaje, mutane suka fara yi masa laƙabi da “Kotal”, wato mutumin da ba a iya kayarwa.

Sunansa ya bazu daga ƙasar Hausa zuwa yankunan Gande, Matankari har zuwa Gao, saboda irin ƙwarewar da yake nunawa a fagen jarumtaka.

Aurensa:

Lokacin da ya kai shekarun aure, labarin jarumtarsa ya isa kunnen Sarkin Arewan Matankari Bagaji, wanda ya aurar masa da ‘yarsa mai suna Lame. Ita ce ta haifa masa ‘ya’yansa na farko.

Shigarsa rundunar Songhai:

Daga baya Muhammadu Kanta ya shiga rundunar mayaƙan Sarkin Daular Songhai, Muhammadu Askiya Toure, ɗaya daga cikin manyan daulolin Afirka a lokacin.

Saboda ƙwarewarsa wajen yaƙi da shugabanci, cikin ƙanƙanin lokaci ya zama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin rundunar Askiya Toure.

Ya jagoranci yaƙe-yaƙe da dama a yankuna daban-daban, ciki har da Agadez, inda aka samu gagarumar nasara tare da kwaso ganima mai yawa.

Yadda aka naɗa shi gwamnan Kabi:

Bayan nasarorin da ya samu a fagen fama, Askiya Toure ya naɗa Muhammadu Kanta a matsayin gwamnan yankin Kabi domin kula da harkokin mulki da tsaro.

A lokacin yana gudanar da mulki cikin hikima da adalci, abin da ya ƙara masa farin jini a tsakanin jama’a.

Rikicin rabon ganima:

Riwayoyi sun ce bayan ɗaya daga cikin manyan yaƙe-yaƙen da aka yi, aka gudanar da rabon ganima tsakanin mayaƙa.

Muhammadu Kanta da mutanensa sun ji cewa rabon da aka ba su bai yi daidai da irin gudunmawar da suka bayar ba. Saboda haka ya nemi a sake duba rabon domin a yi adalci.

Sai dai wasu masu neman tayar da fitina suka rinjayi Askiya Toure da cewa Muhammadu Kanta yana shirin yin tawaye.

Wannan zargi ya lalata kyakkyawar dangantakar da ke tsakaninsu.

Kafuwar Daular Kabi:

Bayan tattaunawa ta ci tura, Muhammadu Kanta ya yanke shawarar ballewa daga Daular Songhai tare da kafa mulki mai cin gashin kansa.

Wannan mataki ne ya haifar da kafuwar Daular Kabi, wadda daga baya ta zama ɗaya daga cikin manyan daulolin yankin Sudan ta Yamma.

Yaƙin Karina:

Ballewar Muhammadu Kanta ta jawo mummunan yaƙi tsakaninsa da tsohon ubangidansa Askiya Toure.

An gwabza wannan yaƙi ne a yankin Karina, da ke cikin yankin Tillabéri na Jamhuriyar Nijar ta yanzu.

Duk da ƙarfin rundunar Songhai, Muhammadu Kanta ya samu nasarar kare sabon mulkinsa.

Wannan nasara ce ta tabbatar da ‘yancin Daular Kabi, tare da buɗe sabon babi a tarihin siyasar yankin.

Za mu ci gaba a mako mai zuwa.

By ukarofi

Leave a Reply