Kotun Tarayya da ke Gusau ta ɗage sauraron ƙarar zaɓen fidda gwani na sanatan APC

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau.

Kotun Tarayya da ke zama a Gusau a ranar Talata ta ci gaba da sauraren ƙarar da Dr. Sani Abdullahi Shinkafi ya shigar, inda yake ƙalubalantar sakamakon zaɓen fidda gwani na jam’iyyar All Progressives Congress, APC, na mazaɓar Sanatan Zamfara ta Arewa.

A cikin ƙarar, Dr. Shinkafi yana neman kotun ta soke zaɓen fidda gwanin da ta ayyana Sanata Sahabi Ya’u Ƙaura a matsayin wanda ya yi nasara.

Dr. Shinkafi ya maka hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC, da jam’iyyar APC don neman haƙƙin sa.

Dr. Shinkafi ya zargi cewa ba a gudanar da zaɓen fidda gwanin yadda ya kamata ba, kuma an yi maguɗi a cikin tsarin zaɓen fidda gwanin na kujerar Majalisar Dattawa shiyyar Zamfara ta Arewa a zaɓen da ya gabata.

Lauyan mai ƙara, Barr. Bello Galadi, ya shaida wa manema labarai bayan zaman kotun cewa an kawo ƙarar ne domin ci gaba da saurara da kuma sauraron wasu batutuwa na farko.

A cewarsa, kotun ta ɗage shari’ar zuwa 28 ga Yuli, 2026 domin karɓar jawabai na ƙarshe na ɓangarorin biyu da kuma gabatar da takardun hujjoji na ƙarshe.

“Mun shigar da takardu guda huɗu na martani a gaban kotu kuma uku daga cikinsu kotu ta amince da su,” inji Barr. Galadi.

“Muna gode wa kotu mai daraja bisa amincewa da uku cikin takardu huɗu, kuma muna da ƙwarin gwiwa cewa adalci zai yi aiki a ƙarshe.”

Ɗagewar ta ba ɓangarorin biyu dama ne su gabatar da jawabansu na ƙarshe a rubuce kafin kotu ta yanke hukunci kan ƙorafe-ƙorafen farko da kuma ƙarar gaba ɗaya.

By ukarofi

Leave a Reply