
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wani mummunan hatsarin kwale-kwale ya auku a yankin Malamawa ta ’Yan Dutse da ke Ƙaramar Hukumar Ringim a Jihar Jigawa, inda mata da yara Sama da 40 suka nutse a cikin ruwa.
Bayanan farko sun nuna cewa mutum ɗaya ya rasa ransa, yayin da har yanzu jami’an ceto tare da mazauna yankin ke ci gaba da lalubo wasu fasinjojin da ba a gano inda suke ba. An kuma yi nasarar ceto wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa.
Har zuwa wannan lokaci, ba a bayyana musabbabin kifewar kwale-kwalen ba, kuma hukumomin da abin ya shafa sun ce suna ci gaba da gudanar da bincike tare da tattara sahihan bayanai kan adadin waɗanda suka mutu da kuma waɗanda aka ceto.
Ana sa ran za a fitar da cikakken bayani daga hukumomi bayan kammala aikin ceto da binciken da ake yi.
