Majalisar Wakilai ta fara bincike yayin da CBN ya tabbatar da buɗe asusu ga hukumar bogi da amincewar AGF

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Babban Bankin Nijeriya CBN, ya shaida wa ƙwarya-ƙwaryar kwamitin binciken shari’ar lamarin hukumar bogi ta PFIPC na Majalisar Wakilai cewa ya samu sahalewar ofishin Akanta Janar na Ƙasa (OAGF) domin buɗe asusu guda biyu ga hukumar.

Hakan na zuwa ne bayan da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) a ranar Litinin ta gayyaci Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila domin amsa wasu tambayoyi kan zarge-zargen da Shugaban Hukumar bogin, Adeyemi Adeniyi ya yi akansa game da al’amarin.

Adeniyi ya yi zargin cewa ya ba wa Gbajabiamila Naira miliyan 400 ta hannun marigayi Babatunde Dolapo Tanimola domin samun naɗa shi a muƙamin. Haka kuma ya yi zargin cewa shugaban ma’aikatan fadar ya nemi a ba shi kaso 48 na kyautar biliyan N27.3 da ake neman karɓa daga hannun gwamnati.

A nasa ɓangaren, Gbajabiamila ya musanta dukkan waɗannan zarge-zargen, inda har ta kai ga ya shigar da ƙarar zargin ɓata masa suna na neman a biya shi diyyar biliyan N15 akan Adeniyi.

An shigar da badaƙalar PFIPC ne bayan gano cewa an ware mata sama da biliyan N1.3 a Kasafin 2026 da aka amince da shi duk da cewa akwai alamar tambaya akan halascinta a shari’ance da kuma samuwar ta.

Bincike ya nuna cewa, ana zargin Adeniyi da samun amincewar ɗaukar ma’aikata guda 300, da samun ofishi a sakatariyar tarayya da ke Abuja da kuma buɗe asusun banki a CBN.

Saidai, OAGF ya trije akan cewa PFIPC ba ta da asusu a babban bankin, batun da ya ci karo da iƙirarin cewa Adeniyi ya yi amfani da wasu takardun bogi ne wajen samun asusun bankin.

Da yake jawabi a gaban kwamitin Majalisar Wakilan a madadin Gwamnan CBN, wani darakta mai suna Hamisu Abdullahi, ya bayyana cewa babban bankin ya yi aiki ne da iko a hukumance daga OAGF na buɗe asusu biyun ga PFIPC.

A cewarsa, an buɗe asusu biyun ne, ɗaya a Dalar Amurka, ɗayan kuma a Fam (Pound Sterling) a ranar 30 ga Yuli, 2025.

Ya bayyana cewa, asusun sun kasance ba sa aiki saboda hukumar ba ta samar da wasu takardun ba a hukumance da za su sanya su fara aiki.

By Babaji