
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Tsaro ta Farin kaya DSS, ta shirya ɗaukaka ƙara akan hukuncin ɗaurin rai-da-rai da Babbar Kotun Tarayya ta yanke wa jagororin ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru biyu a ranar Litinin, 20 ga Yuli, 2026.
Mai Shari’a Emeka Nwite ya yanke hukuncin ne jim-kaɗan bayan da Mahmud Usman da ake kira Abu Bara’a ko Abbas ko kuma Mukhtar da Abubakar Abba da aka sani da Mahmud al-Nigeri/Malam Mamuda, wanda shi ne mataimaki kuma jagoran mayaƙa suka amsa hannu a laifuka guda 32 masu alaƙa da ta’addanci.
Saidai, bayan kammala zaman hukuncin, wani babban jami’in DSS ya bayyana cewa, ɗaurin rai-da-rai da aka yanke musu ya yi sauƙi akan laifukan da aka zarge su da aikatawa.
Ya ce, waɗanda aka yanke wa hukuncin suna dab da amsa hannu a tuhume-tuhumen da ake musu ne sai suka sauya ƙudirinsu jim-kaɗan bayan wasu mutane da ake zargin ‘yan Ansaru ne sun yi awon-gaba da ɗalibai da malamai a Oriire, Jihar Oyo.
A cewar jami’in, barin mutane biyun su tafi da hukuncin ɗaurin rai-da-rai zai zama suka ga shari’a musamman bisa la’akari da kisan gillar da aka yi wa malaman Oriire biyu a hannun ‘yan ta’adda.
Don haka ya ce kasancewar suna ganin hukuncin ba zai wadatar ba ga iyalan malaman ya sa za su ɗaukaka ƙara akan al’amarin.
