Nehemiah Danjuma: Kurman farko da ya zama lauya a Arewa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

An rantsar da matashi, Nehemiah Danjuma a matsayin lauya a Nijeriya, inda ya kafa tarihi a matsayin mutum na farko mai matsalar ji, wato kurma, daga Arewacin ƙasar da aka rantsar domin fara aikin lauya.

Matashi Danjuma, ɗan asalin Jihar Kaduna daga ƙaramar Hukumar Jaba, ya kammala karatun digirin farko na fannin Shari’a da sakamako na Second Class Upper a Jami’ar Ilorin. Daga bisani ya kammala shirin Bar Part II a harabar Abuja ta Makarantar Koyon Aikin Lauya ta Nijeriya.

Da yake sanar da wannan gagarumar nasara a shafinsa na ɗ, Danjuma ya rubuta cewa: “Kurma na farko daga Arewacin Nijeriya da aka rantsar. An kafa tarihi.”

Nasararsa ta samu yabo daga sassa daban-daban, inda mutane da dama suka jinjinawa jajircewarsa da irin ƙalubalen da ya shawo kansu kafin ya zama cikakken lauya.

ɗaya daga cikin abokansa na kusa a Makarantar Koyon Aikin Lauya, Chukwu Nzubechukwu, ya bayyana cewa har ya koyi maganar kurame domin samun sauƙin mu’amala da Danjuma a lokacin karatunsu.

Ya ce, jajircewar Danjuma ta kasance abin ƙarfafa gwiwa gare shi, yana mai nuna fatan ganin ya yi fice a harkar aikin lauya.

Danjuma ya bayyana cewa a shekarar 2017 an fara ba shi gurbin karantar Primary Education Studies a Jami’ar Ilorin, amma bai karɓa ba. Ya sake neman gurbi a shekara ta gaba, inda aka ba shi damar karantar fannin shari’a. Baya ga nasarorin da ya samu a fannin ilimi, Danjuma ya shahara wajen fafutukar kare haƙƙin masu nakasa da kuma jagorancin matasa.

A lokacin da yake Jami’ar Ilorin, ya wakilci ɗalibai masu nakasa a matsayin Sanata na ƙungiyar ɗalibai (Students’ Union). Haka kuma ya yi wa’adi biyu a matsayin Shugaban ƙasa na ƙungiyar ɗalibai Kurame ta Nijeriya (NANDS).

A lokacin shugabancinsa ne aka gudanar da taron ƙasa na farko na ƙungiyar a shekarar 2023, aka ƙaddamar da mujallar NANDS, sannan aka karrama shi da lambar yabo ta gagarumar hidima. Ayyukansa na fafutukar kare haƙƙin masu nakasa sun kai shi matakin ƙasa da ƙasa, inda ya kasance Mai Ba Matasa Shawara Kan Ci Gaban ɗan Adam a shirin European Union Youth Sounding Board a Nijeriya tsakanin 2021 da 2024.

Har ila yau, ya samu shiga shirin Coelho Law Fellowship na Loyola Law School da ke Los Angeles, inda ya samu horo na musamman kan dokoki da manufofin kare haƙƙin masu nakasa. A lokacin karatunsa a Makarantar Koyon Aikin Lauya ta Nijeriya, Danjuma ya yi aikin horaswa a Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya da kuma Ofishin Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, inda ya samu ƙwarewa kan binciken shari’a, rubuta takardun doka da kuma gudanar da shari’u.

Bayan an rantsar da shi a matsayin lauya, Danjuma ya gode wa Muryar Masu Nakasa saboda ɗaukar nauyin kuɗin mai fassara masa magana, sannan ya yabawa gidauniyar JASAN bisa ba shi cikakken tallafin karatu a Makarantar Koyon Aikin Lauya. Ya bayyana wannan nasara a matsayin babban mataki a rayuwarsa, yana mai cewa yana fatan bayar da gudunmawa mai ma’ana ga ci gaban harkar shari’a a Nijeriya.

A halin yanzu, Danjuma shi ne Jagoran Shirye-shirye na Muryar Masu Nakasa, inda yake jagorantar shirye-shiryen wayar da kai, kare haƙƙin masu nakasa da bunƙasa manufofin tabbatar da kowa ya samu dama ba tare da wariya ba.

By ukarofi