
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila ya bayyana a gaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC ) don amsa wasu tambayoyi akan zargin sa da hannu a lamarin hukumar bogi ta PFIPC.
Rahotanni sun bayyana cewa, Gbajabiamila ya amsa gayyatar ICPC ne a ranar Litinin, inda aka masa wasu tambayoyi a game da binciken da ake gudanarwa kan ayyukan PFIPC da aka bayyana a matsayin ta bogi.
Lauyansa, Jiti Ogunye ne ya bayyana haka a wata sanarwa, inda ya ce shugaban ma’aikatan ya bayar da cikakken haɗin kai ga masu bincike bayan Shugaba Bola Tinubu ya umarci a yi bincike mai zurfi akan al’amarin.
A cewar Ogunye, Gbajabiamila ya je ofishin ne tun da mislain ƙarfe 3 na yamma, inda bayan kammala ganawa da masu binciken na ICPCn ne sai ya koma bakin aiki don cigaba da gudanar da harkokin ayyukan da aka ɗora masa.
Hakan na zuwa ne yayin da aka faɗaɗa bincike don gano haƙiƙanin al’amarin PFIPC, bayan al’ummar ƙasa sun koka akan samuwa da kuma ayyukanta.
A ranar 2 ga Yuli ne Shugaba Tinubu ya umarci ICPC ta gudanar da bincike mai zurfi akan al’amarin tare bayar da ba’asin abin da ta gano acikin kwana 30, kamar yadda kakakinsa Bayo Onanuga ya bayyana.
