Ina amfani da wannan dama wajen isar da wata ƙaramar shawara ga mai girma shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote.
Na ji cewa kamfanin ya fito da wata tsari da ke ƙarfafa jama’a su kai rahoton duk direban motar kamfanin da ya karya dokokin hanya, tare da alƙawarin ba da tukuicin har naira dubu d
Dari biyar (N500,000) ga wanda ya bayar da sahihin bayani.
Wannan tsari abin yabawa ne, domin zai taimaka wajen rage haɗurra da kuma tabbatar da cewa direbobin kamfanin suna bin ƙa’idojin tuƙi. Sai dai ina da wata ƙaramar shawara: ya kamata a yi taka-tsantsan wajen tantance duk wani rahoto da ake samu.
Dalili kuwa shi ne, akwai yiwuwar wasu mutane su yi amfani da wannan dama wajen yi wa direbobi aarya ko sharri saboda hassada, sabani ko bambancin ƙabila, domin kawai su sami tukuici ko su cutar da wani. Don haka, ya dace kamfanin ya tabbatar da cewa an gudanar da cikakken bincike tare da samun gamsassun hujjoji kafin a ɗauki mataki kan kowane rahoto.
Ina fatan za a yi la’akari da wannan shawara domin kada yunƙurin gyara ya zama sanadin zaluntar marasa laifi.
Allah Ya taimaki Alhaji Aliko Dangote, Ya albarkaci ma’aikatan kamfaninsa, tare da ɗaukaka Nijeriya. Amin.
Daga MUKHTAR IBRAHIM SAULAWA a Jihar Katsina.07066434519/08080140820.
