An dakatar ba basarake bisa zargin shiga harkokin siyasa a Kebbi

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Karamar hukumar Kalgo da ke jihar Kebbi ta sanar da dakatar da Alhaji Kabir Usman daga matsayin sa na magajin garin Nayilwa.

Wannan yana ƙunshe ne a cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannun sakataren ƙaramar hukumar Kalgo Umar Faruk Sama’ila a madadin shugaban ƙaramar hukumar ranar 11 ga wannan watan na Oktoba.

Takardar ta bayyana cewa an dakatar da basaraken ne bisa ga zarge-zargen tsunduma a cikin harkokin siyasa da ya saɓa wa dokar masarauta.
Har wa yau takardar ta bayyana cewa an naɗa kwamitin bincike kan wannan lamarin kafin ɗaukar mataki na gaba.
Wakilin mu ya nemi jin ta basaraken ta wayar tarho sai dai haka ba ta samu ba saboda wayar sa a kashe amma dai wani mutum daga garin ya bayyana cewa akwai yiyuwar siyasa ce ko kuma waɗansu mutane ne da ke ganin idan aka bi ta wannan hanyar ko da kage a ka yi masa suna iya samun nasara kan sa domin su sami sarautar.

Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da wannan gwamnatin ta dakatar ko tsige sarki ba saboda ko a baya an tsige uwayen ƙasa uku tare da bayar da gargadi ga wadansu da kuma waɗansu sassan jihar.

By ukarofi

Leave a Reply