
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 na jam’iyyar Allied Peoples’ Movement (APM), Seyi Makinde ya ci alwashin zai yi wa’adin shekaru huɗu ne kaɗai a mulki muddin ya lashe zaɓen. Wannan ya biyo bayan irin iƙirarin da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar (NDC), Peter Obi ya yi a baya yayin nuna damuwa kan kewayawar mulki tsakanin arewa da kudancin Nijeriya.
Makinde ya bayyana haka ne a ranar Asabar yayin wani zama da masu ruwa da tsakin APM a Yola, Jihar Adamawa, inda ya yi alƙawarin dawowa da martabar ƙasar da magance matsalolin rashin tsaro, talauci, rashin wadatar wutar lantarki da wasu ƙalubale da al’ummar Nijeriya suke fuskanta. Ya ce gwamnatinsa za ta kasance mai miƙa mulki ga wani ɓangare domin haɗin kan ƙasa. “Gwamnatinmu ba za ta jima sama da shekara huɗu ba. Kuma za ta dama da kowane ɓangare,” inji Makinde.
A baya ne dai Obi, wanda kuma ɗaya ne daga cikin ‘yan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, ya yi alƙawarin yin wa’adi guda idan ya ci zaɓe a 2027, yana mai cewa ba zai ƙara ko da kwana guda ba a ofis koda a halin tsananin matsi.
Makinde ya bayyana cewa, gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen warware matsalolin da suke addabar Nijeriya, sauraron koken ‘yan ƙasa da kauce wa siyasantar da lamuran da suka shafi walwalarsu.
Ya kuma caccaki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan gaza cika alƙawuran da ta ɗauka yayin yaƙin neman zaɓe, musamman a ƙoƙarinta na warware matsalolin lantarki da sassan Nijeriya ke fuskanta a tsawon lokaci.
