Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta buɗe zagayen bayar da lasisin haƙo albarkatun man fetur na shekara ta 2026, inda ta fitar da filayen haƙar mai 40 da suka haɗa da na tsandaurin ƙasa, ruwa maras zurfi da kuma ruwa mai zurfi domin jawo sabbin masu zuba jari cikin harkar haƙo mai da iskar gas.
Hukumar Kula da Harkokin Haƙowa da Tace Man Fetur ta Nijeriya (NUPRC) ce ta sanar da fara zagayen lasisin a ranar Talata, inda Babbar Daraktar Hukumar, Oritsemeyiwa Eyesan, ta ce an ɗauki matakin ne bayan samun amincewar Shugaban ƙasa Bola Tinubu da Ministan Albarkatun Man Fetur.
Eyesan ta bayyana hakan ne a jawabinta na rufe taron bikin cikar hukumar shekaru biyar da aka gudanar a Abuja.
Ta ce, za a bai wa masu zuba jari da ke da ƙwarewar fasaha, ƙarfin kuɗi da kuma cikakkiyar niyyar bunƙasa albarkatun man fetur na Nijeriya damar samun filayen da aka fitar.
“Wannan zagaye ya ƙunshi filayen mai 40 da suka bazu a ƙasa, ruwa mara zurfi da ruwa maras zurfi. Suna buɗe wa masu zuba jari masu ƙwarewar fasaha, ƙarfin kuɗi da kuma, fiye da komai, jajircewar bunƙasa albarkatun man fetur na Nijeriya,” inji Eyesan.
Shugabar NUPRC ta ce zagayen lasisin na 2026 zai fi mayar da hankali kan gaskiya, sahihancin matakai, da kuma bai wa duk masu neman lasisi dama cikin adalci. Ta ce sabbin ƙa’idojin za su tilasta wa duk wani mai neman lasisi bayyana ainihin mutanen da suka mallaki ko ke da rinjaye a kamfaninsa, yayin da za a ƙara bayyana yadda aka tantance masu neman lasisin da kuma sakamakon aikin. Eyesan ta ce hukumar ta yi amfani da shawarwarin da Hukumar Kula da Gaskiya a Harkar Ma’adinai ta Nijeriya (NEITI) ta bayar bayan gudanar da bitar zagayen bayar da lasisin na shekarun 2022 zuwa 2024.
A cewarta, NEITI ta gano cewa matakan da aka bi a baya sun kasance na ƙwarewa, gaskiya da kuma bai wa masu ruwa da tsaki dama, sai dai ta gano wasu fannoni da ke buƙatar ingantawa.
Daga cikin abubuwan da NEITI ta bayar da shawarar a inganta akwai yadda ake tantance masu neman lasisi, bayyana sakamakon tantancewar, bai wa jama’a damar samun bayanan tayin lasisi da kuma bayyana ainihin masu mallakar kamfanonin. Ta ce hukumar ta amince da shawarwarin, kuma za ta aiwatar da su a zagayen na 2026.
Shugabar NUPRC ta kuma jaddada cewa ba za a sake raba filayen man fetur bisa shawarar jami’an gwamnati kawai ba, domin Dokar Masana’antun Man Fetur ta 2021 ta tanadi cewa dole ne a yi gasa wajen bayar da lasisin binciken man fetur da kuma lasisin haƙar man fetur.
