Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
’Yan adawa da shugabannin jam’iyyun siyasa a ƙasar Kenya sun ƙara matsa wa gwamnatin Shugaba William Ruto lamba kan abin da suka bayyana a matsayin rashin cikakken bayani da gaskiya game da shirin gina matatar mai da masana’antar sinadaran man fetur ta Dangote a Lamu. Ana ƙiyasta darajar aikin da kusan Sh2 tiriliyan, kwatankwacin dala biliyan 16.
Shirin haɗin gwiwar da ɗan kasuwar Nijeriya, Aliko Dangote, da Shugaba Ruto suka ƙaddamar a ranar 30 ga Satumba, 2026, ya jawo cece-kuce kan tsarin mallakar kamfanin da zai gudanar da aikin a Kenya, kaso da gwamnatin Kenya ke shirin mallaka, yadda aka ware filayen aikin, yiwuwar amfani da dukiyar gwamnati wajen zuba jari da kuma irin amfanin da ’yan Kenya za su samu.
Gwamnatin Kenya ta ce aikin na da nufin ƙarfafa tsaron makamashi, samar da ayyukan yi da kuma bunƙasa tattalin arzikin ƙasar da yankin Gabashin Afirka baki ɗaya. ɗaya daga cikin waɗanda ke neman gwamnati ta yi bayani shi ne jagoran Jam’iyyar People’s Party of Kenya (PPK), Ndindi Nyoro, wanda ya bai wa gwamnati wa’adin kwanaki 14 da ta bayyana cikakken tsarin masu hannun jarin kamfanin Dangote East African Refinery, bayanan yarjejeniyar filayen da aka ware wa aikin da kuma ko za a yi amfani da Asusun Kayayyakin More Rayuwa na ƙasa wajen gudanar da zuba jarin.
Nyoro ya ce tsarin mallakar aikin batu ne da ya shafi muradun jama’a, don haka ’yan Kenya na da ’yancin sanin waɗanda suka mallaki kamfanin da zai gudanar da matatar, yadda aka raba hannun jarin, kaso nawa gwamnati za ta mallaka da kuma ko an ware wani kaso ga jama’a.
Ya kuma zargi gwamnatin Ruto da gudanar da wasu abubuwa cikin ɓoye, musamman kan yadda take shirin samar da kuɗin kaso 10 cikin 100 da za ta mallaka a aikin ta hanyar Asusun Kayayyakin More Rayuwa na ƙasa.
Nyoro ya ce bai kamata Shugaba Ruto ya fusata ba idan ’yan Kenya suka nemi bayani kan yarjejeniyar. Ya buƙaci gwamnati ta wallafa cikakken jerin masu hannun jarin Dangote East African Petroleum, tare da bayyana yadda aka raba hannun jarin da kuma kaso da gwamnati za ta mallaka, da duk wani kaso da aka ware wa jama’a.
Nyoro ya kuma yi zargin cewa tsarin mallakar kamfanin na iya ɓoye wasu muradun mutanen da ke da alaƙa da gwamnati. “’Yan Kenya suna son ganin jerin masu hannun jarin Dangote East Africa Petroleum. Idan suka ga wasu masu hannun jari suna kiran kansu mutanen UAE ko Dubai, mu mun san cewa ba mutanen Dubai ba ne; mun san cewa mutum ne da ke nan Kenya mai suna William Ruto da yake tafiya da dukiyar ’yan Kenya,” inji shi.
Gwamnatin Kenya ta sanar da shirin mallakar kaso 10 cikin 100 na matatar mai da ake son ginawa a Lamu. Shugaba Ruto ya ce za a samar da kuɗin jarin ne ta hanyar amfani da kadarorin gwamnati, ciki har da filaye, da kuma Asusun Kayayyakin More Rayuwa na ƙasa.
“Ba ma son a ba mu komai kyauta. Za mu yi amfani da kadarorinmu, ko filaye ko wasu kadarori, sannan mu yi amfani da Asusun Kayayyakin More Rayuwa na ƙasa wajen zuba jari a wannan matatar,” inji Ruto a baya.
Sai dai duk da sanarwar cewa gwamnati za ta mallaki wani kaso a aikin da aka kiyasta darajarsa ta kai Sh2.2 tiriliyan, har yanzu ba a bayyana dalla-dalla yadda za a tsara da aiwatar da tsarin samar da kuɗin jarin ba. Nyoro na buƙatar gwamnati ta bayyana ko filayen da Kenya za ta bayar za a mayar da su wani kaso na hannun jari, da kuma adadin kuɗin da za a kimanta darajar waɗannan filaye da shi.
Kwamitin da ke kula da Asusun Kayayyakin More Rayuwa na ƙasa bai bayyana cikakken bayani kan tsarin ba. Haka kuma, shirin shigar da sama da Sh200 biliyan cikin asusun ta hanyar sayar da hannun jarin kamfanin sadarwa na Safaricom da gwamnati ke riƙe da su ya gamu da matsalar shari’a bayan kotuna sun dakatar da cinikin.
