Dangote ya dakatar da sayar da fetur ga masu shigo da shi

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Matatar Man Fetur ta Dangote ta dakatar da sayar da man fetur ga manyan ’yan kasuwar man fetur da ke shigo da kayayyakin man fetur daga ƙasashen waje zuwa Nijeriya, lamarin da ya ƙara tsananta taƙaddamar da ke tsakanin matatar da masu shigo da fetur.

Wani jami’in matatar ya tabbatar da matakin, inda ya ce matatar ba za ta cigaba da sayar da fetur ga ’yan kasuwar da ke haɗa man Dangote da fetur da suka shigo da shi daga ƙasashen waje ba.

“Ba ma sayar da fetur ga waɗanda ke shigo da shi, saboda suna ƙoƙarin haɗa manmu mai inganci da na shigo da shi wanda ingancinsa ya yi ƙasa sosai,” inji jami’in, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda ba shi da izinin magana da manema labarai.

Wata majiyar kuma ta ce matatar yanzu ta fi mayar da hankali wajen sayar da fetur ga ’yan kasuwa masu zaman kansu, musamman mambobin ƙungiyar ’Yan Kasuwar Man Fetur ta ƙasa (IPMAN), da kuma sauran ’yan kasuwar da ba a san suna shigo da fetur daga ƙasashen waje ba. “Yanzu muna sayar da fetur ga ’yan kasuwa masu zaman kansu da sauran waɗanda ba sa shigo da man fetur,” inji majiyar.

An fahimci cewa wannan mataki ne ya sa wasu daga cikin ’yan kasuwar man fetur suka garzaya kotu domin neman umarni da zai tilasta wa Hukumar Kula da Harkokin Haƙowa da Tace Man Fetur ta ƙasa (NMDPRA) ta ci gaba da ba su lasisin shigo da man fetur. ’Yan kasuwar sun nuna fargabar cewa za su iya rasa abin da za su sayar idan aka hana su shigo da fetur, musamman a lokacin da Matatar Dangote ta dakatar da sayar musu da man.

Tun da farko dai Dangote ya yi barazanar dakatar da hulɗar kasuwanci da masu shigo da fetur, bisa zargin cewa suna haɗa man fetur ɗinsa mai darajar Euro 5 da man da suke shigo da shi daga ƙasashen waje. Matatar ta ce irin wannan aiki na iya sa ya yi wahala a bambance man da ta samar kai tsaye da wanda wasu ɓangarori suka sake haɗawa ko sarrafa shi.

A watan da ya gabata, matatar ta ce ba ta fahimci dalilin da zai sa ta kashe makudan kuɗaɗe wajen samar da man fetur mai inganci ga ’yan Nijeriya, sannan a haɗa shi da man da aka shigo da shi wanda ba a tabbatar da ingancinsa ba, daga nan kuma a danganta sakamakon ga matatar.

Sai dai masu shigo da man fetur da sauran ’yan kasuwar sun yi tir da matakin matatar, suna bayyana shi a matsayin yunƙurin hana shigo da fetur daga ƙasashen waje. Sun kuma ƙalubalanci Matatar Dangote da ta gabatar da hujjar cewa fetur ɗin da ake shigowa da shi Nijeriya bai kai matsayin ingancin da doka ta tanada ba.

Wasu daga cikin ’yan kasuwar, waɗanda suka nemi a sakaya sunayensu, sun zargi Dangote da ƙoƙarin toshe hanyar shigo da fetur daga ƙasashen waje. “Mun san abin da Dangote yake ƙoƙarin yi. Yana son kawai ya hana shigo da fetur,” inji ɗaya daga cikin ’yan kasuwar.

Ya ce kamfanin da ke sayar da fetur ba shi da ikon hana mai saye haɗa man da ya saya daga wurinsa da wanda ya saya daga wani mai samar da man. Ya yi misali da yadda direba zai iya sayen fetur daga gidajen mai daban-daban.

“Misali, ka sayi fetur a gidan mai na TotalEnergies, sannan ka ci gaba da tafiya, fetur ɗin ya kusa ƙarewa, sai ka sayi wani a gidan mai na MRS. Shin TotalEnergies za ta ce kada ka haɗa man da ka saya a wurinta da na MRS? A’a, ba za ta iya ba. Ban fahimci abin da Matatar Dangote take ƙoƙarin yi ba,” inji shi.

Wani ɗan kasuwar man fetur ya kuma ce Gwamnatin Tarayya na da alhakin tabbatar da isasshen man fetur a kasuwa tare da kare masu amfani da shi. Ya ce, shigo da fetur daga ƙasashen waje na ci gaba da zama dole a duk lokacin da samar da man cikin gida bai wadatar da buƙatar ƙasa ba.

Mataimakin Shugaban ƙungiyar ’Yan Kasuwar Man Fetur ta ƙasa (IPMAN), Hamed Fashola, ya ce Matatar Dangote na zaɓar waɗanda take sayar wa fetur, saboda ba duk manyan ’yan kasuwar man fetur ne ke shigo da shi daga ƙasashen waje ba. “Ban san iyakar gaskiyar wannan bayanin ba; abin da na sani shi ne Dangote yanzu yana sayar wa IPMAN ne kawai. Amma ina ganin bayanin da nake da shi shi ne matatar tana zaɓar waɗanda take sayar wa, musamman waɗanda ke cikin shigo da man fetur. Ba kowa ne ke shigo da man ba,” inji Fashola.

Yayin da yake bayani kan yadda mambobin IPMAN ke sayen fetur a kasuwa, Fashola ya ce ’yan kasuwar suna da ’yancin sayen man daga duk inda suka samu farashi mafi sauƙi, ko daga matatun cikin gida ko masu shigo da shi.

By ukarofi

Leave a Reply