Hukumar ƙwallon ƙafar Portugal ta tabbatar da lokacin dawowar Ronaldo cikin tawagar ƙasar

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Zakaran ɗan ƙwallon ƙafar duniya kuma ɗan ƙasar Portugal, Cristiano Ronaldo ya shirya koma wa cikin tawagar ‘yan wasan ƙasar a watan Nuwamba, bayan dakatarwar da hukumar ƙwallon ƙafar ƙasar ta masa.

An faɗaɗa raɗe-raɗin makomar ɗan wasan ne bayan ya bar cikin tawagar yayin wasannin gasar Nations League a watan Satumba, lamarin da ya haifar da jita-jitar cewa akwai yiwuwar ya yi ritaya daga buga mata ƙwallo sakamakon rikicin da ya ɓarke tsakaninsa da kociyan Portugal, Jorge Jesus.

Shugaban hukumar ta FPF, Pedro Proenca ya yi watsi da batun yiwuwar ɗan wasan ya yi ritaya, inda ya ce “baki ɗaya ‘yan wasan a haɗe suke. Mu na son Cristiano ya dawo. Ina fatan zai dawo a Nuwamba yayin hutun wasannin ƙasa-da-ƙasa”. Ronaldo zai shafe ƙaramin lokaci na dakatarwar da aka masa bisa barin tawagar Portugal ba tare da izini ba.

A wani ɓangare, Ronaldo a ranar Juma’a, ya zura ƙwallo na 980 a tarihin ƙwallon ƙafarsa a yayin wasan da ƙungiyarsa ta Al Nassr ta yi nasara akan Al Diriyah.

By Babaji

Leave a Reply