Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ƙungiyar narubutan labarin wasanni ta ƙasa (SWAN) reshen jihar Katsina, ta sanya ranar Juma’a, 23 ga watan Oktoba na 2026, da za ta fara gasar ƙwallon ƙafa ta farko tsakanin ma’aikatun gwamnati da hukumomi wanda aka sanya wa sun (Dikko Raɗɗa Inter-Ministerial Football Competition.)
Shugaban ƙungiyar a Katsina Kwamred Nasiru Gide ya bayyana haka bayan ganawa da wakilan ma’aikatu da hukumomin da za su fafata.
Yace ma’aikatu da hukumomi 15 za su fafata a gasar, inda aka raba su zuwa rukuni hudu, domin fafatawa a matakin farko.
A rukuni na A, hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) za ta fafata da ma’aikatar matasa da wasanni,da ma,akatar shirin bunkasa al’umma, da kuma ofishin shugaban ma’aikatan gwamnati, domin neman gurbin zuwa mataki na gaba.
A rukuni na B, akwai hukumar kula da ci gaban jihar Katsina, ma’aikatar ayyuka, rundunar ‘yan sandan Najeriya, da kuma Ofishin sakataren gwamnatin Katsina.
A rukuni na C, hukumar kula da filayen jiragen sama ta tarayya (FAAN) za ta fafata da ma’aikatar yaɗa labarai da ƙungiyar likitoci ta Najeriya (NMA).
A gefe guda kuma, rukuni na D ya ƙunshi ma’aikatar lafiya, jami’ar Umaru Musa Yar’Adua (UMYU), ma’aikatar Ilimin firamare, da kuma rundunar tsaron farar hula ta Najeriya (NSCDC).
Gide ya bayyana cewa an shirya gasar ne domin ƙarfafa haɗin kai da haɗin gwiwa, kyakkyawar mu’amala a tsakanin ma’aikata, da kuma inganta lafiyar jiki tsakanin ma’aikatan gwamnati a ma’aikatu da hukumomin gwamnatin jihar Katsina.
Kwamred Gide , ya yaba wa Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, bisa irin goyon bayan da yake bai wa ci gaban wasanni, da kuma yadda yake nuna himma wajen bunƙasa harkokin wasanni a jihar.
Ya ƙara da cewa SWAN za ta ci gaba da amfani da wasanni a matsayin wata hanya ta karfafa haɗin kai, kyautata alaƙa tsakanin ma’aikatan gwamnati, da kuma ƙarfafa mutane su rungumi rayuwa mai kyau da kula da lafiyarsu.
Ana sa ran wannan gasa ta farko za ta haɗa ma’aikatan gwamnati daga ma’aikatu da hukumomi daban-daban, inda za su fafata cikin yanayi na gasa,zumunci da haɗin gwiwa.
