Paga ta yi gargaɗi kan auren ƙananan yara a Arewa maso Gabas

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe

Wata mai rajin kare haƙƙin mata da ’ya’ya mata, Ambasada Fatima Mohd Paga, ta yi kira da a ɗauki matakan gaggawa domin kawo ƙarshen auren ƙananan yara da cin zarafin jinsi a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Paga, wadda ke kula da ayyukan UN Women a Jihar Yobe, ta ce rashin tsaro da rikice-rikice sun jefa ’ya’ya mata da dama cikin haɗarin fyade, tilasta musu aure da kuma katse karatunsu.

Ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar domin bikin ranar ƙasa da ƙasa ta ’ya’ya mata ta shekarar 2026, mai taken, “A kawar da auren ƙananan yara, a zuba jari ga ’ya’ya mata.”

Ta ce ’ya’ya matan da ke zaune a yankunan da rikice-rikice suka shafa, musamman waɗanda ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai suka sace, sun fi fuskantar barazanar cin zarafi da tilasta musu zama iyaye tun suna ƙanana.

A cewarta, auren ƙananan yara na hana ’ya’ya mata samun ilimi, tare da jefa su cikin haɗarin matsalolin lafiya kamar yoyon fitsari sakamakon nakuda, raunin haihuwa da mutuwar mata yayin haihuwa.

“Bai kamata wata yarinya ta rasa ƙuruciyarta ko makomarta saboda yanayin da ba ta da iko a kansa ba,” in ji ta.

Paga ta yaba da ƙoƙarin Gwamnatin Jihar Yobe na kare haƙƙin yara, musamman ta hanyar dokar haƙƙin yara da Gwamna Mai Mala Buni ya amince da ita.

Sai dai ta jaddada cewa wajibi ne a tabbatar da cikakken aiwatar da dokar domin kare yara daga cin zarafi da tauye haƙƙoƙinsu.

Ta kuma yi kira ga iyaye da shugabannin al’umma da su yi watsi da tunanin cewa ilimantar da ’ya’ya mata ɓata lokaci da kuɗi ne.

“Ilmantar da yarinya ba ɓata lokaci ba ne; zuba jari ne ga makomarta, iyalinta, al’ummarta da ci gaban ƙasa,” in ji ta.

Ta buƙaci gwamnatoci, jami’an tsaro, sarakunan gargajiya da shugabannin addinai, kafafen yaɗa labarai da ƙungiyoyin fararen hula da su haɗa kai wajen kawo ƙarshen auren ƙananan yara, kare ’ya’ya mata daga cin zarafi da tabbatar da samun ingantaccen ilimi.

Paga ta ce bikin ranar ’ya’ya mata bai kamata ya tsaya ga jawabai da shagulgula ba, sai dai ya haifar da matakan da za su tabbatar da tsaron ’ya’ya mata, kare haƙƙoƙinsu da ba su damar cimma burinsu.

Ta jaddada cewa kowace yarinya tana da haƙƙin samun rayuwa cikin aminci, ilimi mai inganci da damar bayar da gudummawa ga ci gaban al’ummarta.

By ukarofi

Leave a Reply