
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ɗan takarar gwamna a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar PDP a Jihar Kano, Muhammad Sani Abacha, ya ayyana cewa jam’iyyar ta shirya sake karɓar mulki a jihar bayan Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta tantance shi a matsayin ɗan takara.
Muhammad Abacha, wanda ya kuma yi wa INEC godiya kan matakin, ya ce har yanzu PDP na nan da ƙarfinta a siyasar Kano kuma ta shirya tattara kan mambobinta a baki ɗaya ƙananan hukumomi guda 44 na faɗin jihar domin samun nasara a zaɓen da ke tafe a 2027.
Ya kuma bayyana godiyarsa ga jagorancin jam’iyyar a matakin ƙasa, jihar Kano, deligets da suka zaɓe shi, masu ruwa da tsaki da mambobin jam’iyyar bisa ƙwarin-gwiwar da suke da shi akansa. Ya bayyana goyon bayan nasu a matsayin tabbatar da yarda ta aiki tuƙuru, shawarwari da ƙoƙarin samar da ci-gaba a Jihar Kano.
Ɗan marigayi tsohon Shugaban Mulkin Sojin ya kuma kirayi mambobin jam’iyyar da su mayar da hankali akan masu zaɓe, yana mai cewa yaƙin neman zaɓen PDP zai karkata ne kan kyawawan fata, damarmaki, gaskiya da adalci, da kuma ci-gaba daga kowane ɓangare.
Kazalika, ya tabbatar wa ‘yan jihar cewa muddin ya lashe zaɓe, zai kafa gwamnatin da za ta riƙa tuntuɓa da neman shawarwari akan al’amuran da suka shafi maslahar al’umma da ƙoƙarin gina shugabanci na gari.
