Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
‘Yan sanda sun daƙile yunƙurin kai hare haren ‘yan bindiga a ƙananan hukumomin Funtua da Musawa tare da ceto shanu guda 15.
Sanarwa ɗauke da sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya fitar,ofishin ‘yan sanda na garin Funtua sun sami bayanin sirri na wucewar ‘yan bindiga da shanu da ake zargi na sata ne suna kan iyakar Funtua zuwa Dandume.
DSP Sadiq ya ce nan take DPO na ofishin da ke Funtua shi da jami’an sa suka fatattaki ‘yan bindigan.
Yan sandan sun sami nasarar ceto wata mata Hafiza Rabi’u da shanu bakwai wanda bayan duba lafiyar ta an miƙa ta ga iyalan ta.
Haka kuma a garin Musawa bayan samun bayani na sirri da ke nuna ‘yan bindigan ɗauke da manyan makamai sun kai hari a ƙauyen Kuru kamar yadda DSP Sadiq ya bayyana.
Ya ce nan take ‘yan Slsanda da haɗin gwiwa na CWC ƙarƙashin DPO na garin Musawa suka bi hanyar har suka gano ‘yan bindigan a kusa da wani daji suna ƙoƙarin gudu.
A nan jami’an su kai galaba a kan ‘yan bindigan da ta kai ma sun ranta a na kare. Jami’an tsaron sun sami nasarar ceto shanu takwai.
Kwamishinan ‘yan sanda CP Ali Umar Fage ya yaba wa jami’an tsaron kan ƙwarewa da jajircewa da suka nuna wajan samun galaba akan ‘yan bindigan.
Ya sha alwashin yaƙar ta’adanci da sauran mayan laifuka a jihar.
