Tare da BILKISU YUSUF ALI, P.hD
Gabatarwa
Ritaya wani mataki ne na rayuwa da kowane ma’aikaci zai iya fuskanta idan Allah Ya ba shi tsawon rai. A mafi yawan lokuta, mutane suna shiryawa ne domin samun aiki, samun albashi da gina iyali, amma ba sa bai wa rayuwa bayan ritaya muhimmancin da ta dace. Wannan rashin shiri kan haifar da matsalolin tattalin arziƙi, damuwa ta tunani, matsalolin lafiya da kuma rashin walwala. Masana ilimin zamantakewa da tattalin arziƙi sun nuna cewa shiryawa tun kafin ritaya yana taimakawa mutum ya ci gaba da rayuwa cikin mutunci, kwanciyar hankali da walwala.
Ma’anar ritaya
Ritaya ita ce daina aiki na dindindin bayan mutum ya kai shekarun da doka ko tsarin aiki ya tanada, ko kuma saboda rashin lafiya ko wasu dalilai. Sai dai ritaya ba tana nufin ƙarshen rayuwa ba ce, illa dai sabon babi ne da ke buƙatar sabon tsari.
Muhimmancin shirya rayuwa bayan ritaya
Shirye-shiryen rayuwa bayan ritaya suna taimakawa mutum wajen samun kwanciyar hankali da
kare mutuncinsa da rage talauci da rage damuwa da ciwon zuciya da ci gaba da amfani da ilimi da gogewarsa wajen hidimar al’umma.
Muhimman abubuwan da ya kamata a shirya
1. Shirin kuɗi (Financial Planning)
Wannan shi ne ginshiƙin rayuwar bayan ritaya. Ya kamata mutum ya riƙa yin tanadi tun yana aiki. Ya rage yawan bashi, ya zuba jari mai aminci ya tanadi kuɗin gaggawa ya tsara yadda zai kashe kuɗinsa.Masana suna ba da shawarar a fara shirin ritaya shekaru 10 zuwa 20 kafin ritaya.
2. Kula da lafiya
Lafiya ita ce babban jari. Ya kamata mai ritaya ya riƙa motsa jiki da cin abinci mai gina jiki da yin gwajin lafiya lokaci-lokaci. Ya kamata duk wanda shekarunsa suka kai na ritaya ya ƙauracewa barin shan taba da giya haka mai ritaya ya kamata yak e samun isasshen bacci.
Cire damuwa da samar da tunani da walwala
Wasu suna shiga damuwa bayan ritaya saboda sun rasa aikin da suka saba wanda suka ɗora rayuwarsu a kai tun tasowarsu. Wannan kaɗai ya isa ya sa damuwa in har ba a shirya ba. Amma a wanda ya shiryawa wannan yanayi yakan sauya damuwar zuwa nishaɗi ta yin wasu ayyuka da za su maye gurbin damuwa.Da farko ana buƙatar karɓar canjin rayuwa da yin hulɗa da mutane da shiga ƙungiyoyin al’umma da yin ayyukan sa-kai da koyon sabbin abubuwa.
4. Cigaba da ilimi
A zamnin yau ba a daina koyo don haka mai ritaya zai iya koyon amfani da kwamfuta da koyon kasuwanci da halartar kwasa-kwasai da yin Rubuce-rubuce da bincike da koyarwa.
5. Samar da sana’a
Ritaya ba tana hana kasuwanci ba ne hasali ma lokaci ce ta neman mafita don haka mai ritaya zai iya noma da kiwo da kasuwanci da bayar da Shawarwari (Consultancy) da horarwa a fagen da yake da ido da yin rubuce-rubuce da ma samar da wata kafa don ƙaruwa a kafafen sada zumunta.
6. Gina dangantakar iyali
Ritaya lokaci ne na ƙarfafa zumunci.Ya kamata mutum ya ba iyalansa lokaci da tarbiyyantar da ‘ya’ya da jikoki da sulhunta ‘yan uwa da tallafawa al’umma.
7 Komawa ga addini
Ga musulmi da kirista, ritaya wata dama ce ta ƙara kusanci da Allah. Don haka duk wanda ya yi ritaya ana sa ran a gay a mayar da al’amuransa ga Allah ta hanyar yawaita ibada da karatun littattafai da sauraron wa’azi da yin sadaka in da hali da hidimar al’umma.
8. Nishaɗi
Wata gaɓa mai muhimmanci ga wanda ya yi ritaya ita ce samar wa kai nishaɗi. Ana son mai ritaya ya ƙirƙirarwa kansa wani nishaɗi ko lokacin walwala da watayawa kamar wasanni da motsa jiki da nishaɗi kallon fina-finai da zuwa cinema ga masu wanda ya saba a baya. Kallon kwallo ko wani wasa da za a wasa kwakwalwa. Sauraron waƙoƙi na ɗebe kewa ko na soyayya ko na jarumta da sauraransu (wannan ya danganta da ɗabi’ar mutum kafin ritaya tun lokacin da ake da ƙuruciya).
9. Tafiye–tafiye
Akan samu wanda a baya yana son yawan tafiye in har mai ritaya yana da wannan ɗabi’a bayan ritaya ya kamata yake ɗan taɓa wa ko don samun sauyin wurin zama na wucin gadi. Wannan ma yana sa mutum ya samu nishaɗi.
Za mu cigaba a mako mai zuwa in sha Allah
