NIHSA ta gargaɗi Kano, Adamawa, Jigawa da wasu jihohi 14 kan yiwuwar ambaliya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Kula da Harkokin Ruwa ta Ƙasa (NIHSA), ta fitar da sanarwar gargaɗi na kwana bakwai akan yiwuwar aukuwar ambaliya a jihohi guda 17 na sassan Nijeriya daga ranar 21 zuwa 27 ga watan Yuli, 2026.

Darakta-Janar na NIHSA, Umar Mohammed, ya ce an ɗauki matakin ne bayan hauhawar matakan ruwa a wasu manyan koguna, lamarin da ka iya haddasa ambaliya a wasu yankuna.

Umar Mohammed ya ce, jihohin da abin ya shafa sun haɗa da Adamawa, Bauchi, Benuwai, Borno, Edo, Gombe, Imo, Jigawa, Kaduna, Kano, Kebbi, Nasarawa, Neja, Filato, Taraba, Yobe da kuma Zamfara.

Ya bayyana cewa, jihar Bauchi ce ke kan gaba wajen fuskantar barazana, inda aka gano al’ummomi 1,841, makarantu 145, cibiyoyin lafiya 101 da kasuwanni takwas na cikin haɗarin aukuwar ambaliya.

Akan haka ne hukumar ta buƙaci gwamnatocin jihohi, hukumomin agajin gaggawa da shugabannin al’umma su ɗauki matakan kariya ciki har da kwashe mazauna yankunan da ke fuskantar haɗari, da tanadar kayan agaji, tare da share magudanan ruwa domin rage illar ambaliya.

Kazalika, ta shawarci jama’a da su riƙa bibiyar sanarwar da hukumar ke fitarwa akai-akai domin ɗaukar matakan kariyar da suka dace da yankunansu.

By Babaji

Leave a Reply