‘Yan sanda sun kama wani ƙasurgumin dillalin miyagun ƙwayoyi a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Yan sanda a Katsina sun samu nasarar kama wani mai suna Ibrahim Usman ɗan shekara 37 da haihuwa yana ɗauke da tabar wiwi.

Kamar yadda jami’in hulɗa da jama’a DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya fitar da sanarwa,an kama wanda ake zargi ɗauke da tabar wiwi a dunƙule har guda 28 a kan Iyakar Mashi zuwa Birnin Kuka a ƙaramar hukumar Mashi.

A yayin gudanar da bincike ya shaida wa yan sanda cewa yana da niyar kaiwa sassa daban na jihar Katsina domin sayarwa, DSP Sadiq ya ce.

Yanzu haka yan sanda na cigaba da bincike da zarar ta kammala za a gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu.

Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar CP Ali Umar Fage ya sha alwashin yaƙi da masu ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a faɗin jihar inda yayi kira ga alummar Jihar da su cigaba da ba jami’an tsaro goyon baya wajen fallasa irin waɗannan miyagun mutane.

By ukarofi

Leave a Reply