
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaban gasar La Ligar ƙasar Sifaniya, Javier Tebas, ya buƙaci Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA), Gianni Infantino da ya gaggauta yin murabus daga muƙaminsa kan abin da ya kira da “ɗaukar matakai masu haifar da cece-kuce” da ke rusa harkar ƙwallon ƙafa.
A wata hira da jaridar ƙasar Italiya La Gazzetta dello Sport, Tebas ya zayyano matsaloli da dama ciki har da hutun shan ruwa, ƙarin lokacin hutun rabin lokaci da ya ba taurarin waƙa damar gabatar da wasa, shiga tsakani kan dakatar da ɗan wasa da kuma buƙatar neman a ƙara adadin ƙasashen gasar Kofin Duniya zuwa 64.
Ya bayyana cewa, Infantino na samun goyon bayan hukumomin ƙwallon ƙafan ƙasashe, wanda hakan ya sa babu wasu ‘yan takara masu ƙarfi da za su kara da shi a muƙamin jagorancin FIFA.
A cewarsa, akwai buƙatar hukumomin ƙwallon ƙafa su sake nazari akan sake zaɓar sa a matsayin jagoran hukumar ƙwallon duniyar a wani karo duba da yadda al’amura a fagen ƙwallon ƙafa suke sauya salo da ke haifar da cece-kuce da rashin amincewa daga wasu ɓangarori na masu ruwa da tsaki a harkar.
