NNPC ya ƙara farashin fetur

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Babban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa NNPCL, ya ƙara farashin litar man fetur a gidajen sayar da man da ke ƙarƙashin ikonsa.

Rahotanni sun nuna cewa kamfanin ya ɗaga farashin daga N1,155 zuwa N1,270 kan kowace lita a Abuja da kewaye, wanda ke nuna ƙarin Naira 115.

Rahotanni sun ce wasu gidajen mai na NNPCL da MRS sun dakatar da sayar da fetur na ɗan lokaci, yayin da sauran gidajen mai suka ƙara farashin sakamakon sauye-sauyen da ke faruwa a kasuwar man fetur.

Karin farashin ya zo ne bayan masu gidajen ajiya da dillalan man fetur sun yi karin farashi sau biyu cikin ƙasa da mako guda, yayin da matatar Ɗangote ta koma sayar da kayayyakin man fetur da dalar Amurka.

Wannan mataki na zuwa ne bayan sauye-sauyen farashin da aka samu a kasuwar man fetur, yayin da wasu masu sayar da mai su ma suka fara daidaita farashinsu.

Ana sa ran ƙarin farashin zai shafi kuɗin sufuri da farashin kayayyaki da ayyuka a Nijeriya.

By Babaji

Leave a Reply