‘Yan sanda ke kan gaba yayin da ICPC ta fallasa ma’aikatan bogi 908 da ƙwato zambar miliyan N942

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ICPC, ta gano cewa akwai ma’aikatan bogi da dama a Rundunar ‘Yan Sanda ta Nijeriya da ma’aikatun gwamnati guda biyar da hukumomin tarayya yayin da take nazari akan albashin ma’aikata.

Shugaban ICPC, Musa Adamu Aliyu (SAN) ne ya bayyana haka yayin da yake magana kan binciken damfara a cikin biyan albashi a hukumomin gwamnatin tarayya.

Hukumar ta ce ta gano ma’aikata ‘yan jabu guda 908 a ma’aikatun gwamnati, sassa da hukumomi aƙalla 50.

Haka kuma, ta dawo da kimanin Naira miliyan 942 da ake zargin an biya a matsayin albashi na damfara.

A cewar ICPC, ma’aikata na bogi suna nufin sunaye na karya da aka saka a jerin ma’aikatan gwamnati domin samun albashi ga wasu mutane ba bisa ƙa’ida ba.

A wasu lokuta, ana zargin jami’ai suna karkatar da albashi ta hanyar saka danginsu ko abokan arziƙi cikin jerin ma’aikata ko da kuwa ba’a ɗauke su aiki ba.

By Babaji

Leave a Reply