Kwamishinan ilimin Katsina ya cigaba da ziyarar makarantun da jarrabawar NECO ke gudana

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

A ƙoƙarin sa na ganin ɗalibai da ke cigaba da zana jarrabawar NECO basu sami wata matsala ba, kwamishinan ilimi a Jihar Katsina Alhaji Yusuf Suleiman Jibiya ya kai ziyarar sa ido a wasu makaratun a cikin garin Katsina.

Makaratun da ɗalibai ke zana jarabawar sun haɗa da Government Senior Secondary School Kofar Kaura (Tudun Matawalle) da Eldan Science and Arabic Academy, Government Day secondary School Kofar Yandaka da School for the Blind sai Sir Usman Nagogo college of Arabic and Islamic studies.

Kwamishinan ya ce mahimmancin ziyarar shine ma’aikatar sa ta gano wuraren da ke neman kulawa cikin gaggawa musamman abin da ya shafi ɗalibai da ke zana jarabawar ta NECO a jihar.

Bayan kammala ziyarar, kwamishinan ya ce ya nuna gamsuwar sa tare da jaddada ƙudirin gwamnatin Katsina na tabbatar da gudanar da Jarabawa mai sahihanci a faɗin jihar.

Ya yaba wa hukumomin makaratun da ya ziyara kan yadda ɗalibai ke zana jarabawar ta bin ƙa’idojin da da hukumar jarabawa ta NECO ta shimfida a ƙasa baki ɗaya.

Alhaji Yusuf Suleiman ya nuna gamsuwa kan yadda ɗalibai ke zana jarabawar cikin natsuwa ba tare da wata matsala ba.

Ya bayana cewa shi da daraktoci na ma’aikatar za su cigaba da wannan ziyarar a sauran sassan jihar domin tabbatar komai ya tafi daidai a makarantun da ake gudanar da jarabawar.

By ukarofi

Leave a Reply